Languages

Sokoto state government said it is open to partnering with public and private organisations

Gwamnatin jahar sokoto tace a shirye take ta hada hannu  da hukumomi na gwamnati da kuma masu zaman kansu domin shigar al’umma acikin ayyukan kawo cigaba.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya fadi hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin daraktan kamfanin Chevron Senator Gbenga Aluko wanda ya kawo masa ziyara a ofishinsa

Aluko wanda yaje fadar  gwamnati domin ya shaidawa gwamnan akan manufar da suke da ita na samar da dakin karatu na ji da fadi  a daya daga cikin makarantinnen sakandire dake nan sokoto

A lokacin da yake jawabi, Aluko yace kamfanin Chevron  a can baya ya taba samar da wani karamar asibitin maganin kirji a asibitin  kwararru na Murtala Muhammad dake nan sokoto,yayinda wasu daga cikin yan asalin jahar sokoto suka amfana da daukar nauyin da kamfanin yayi ga wasu dalibban karatun likitanci da kuma karatun injiniyanci.

Yace kudirin  gina wannan dakin na karatu da suke dashi yana daya daga cikin hanyoyinsu na bada gudummuwa  a fannin ilimi ,inda yace yanzu haka suna gudanar da makamancin wannan aikin domin bunkasa samar da ruwa da kuma kiyon Lafiya a wasu sassa na kasar nan. 

Vision FM 92.1 Sokoto

Theme Colors

Please select the following colors to preview different color schemes of the theme.