Languages

The Federal Ministry of Education has denied report in the media

Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta musanta wani rahoto daga kafafen labarai wanda yake cewa ministan Adamu Adamu ya bayar da umurni zuwa ga jami’oi na soke jarabawar samun gurbin shiga manyan makarantinnen  gaba da sakandire wadda aka riga aka tsara yi.

Ministan acikin wani jawabi mai dauke das a hannun darektan kula da yan jarida da kuma hulda da jama’a acikin ma’aikatar, ya bayyana rahoton a matsayin wanda ba gaskiya ba kuma marar tushe.

Akan haka ministan yayi kira ga jami’oi dasu cigaba da shiryeshiryensu na gudanar da jarabawar kamar yadda aka shata da farko, inda kuma aka janyo hankalin ministan akan wasu makarantinnen da ke karbar fiye da kudi dubu biyu da ake biya, inda ya ayyana wannan lamari a matsayin abinda bai dace ba.

Ministan ya jaddada umurnin  cewa duk makarantar da aka kama tana gudanar da ayyukanta sabanin yadda aka shata zata fuskanci hukunci.

Ya kara da bayar da umurnin cewa wadannan makarantinnen su yi gaggawar mayar ma da daliban kudadensu ,inda ya umurci  ma’aikatar jarabawar ta samun guraben shiga makarantinnen gaba da sakandire das u fito da sunayen wadanda suka saba dokar domin a hukuntasu. 

Vision FM 92.1 Abuja

Theme Colors

Please select the following colors to preview different color schemes of the theme.