Languages

Ministan ma’adinai da karafa Kayode Fayemi ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari bayani

Ministan ma’adinai da karafa Kayode Fayemi ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari bayani akan halin da kamfanin karafa na Ajaokuta dake jihar Kogi da kuma  kamfanin sarrafa Aluminium dake Ikot Abasi ke ciki.

Kamfanin sarrafa aluminum wanda shi kadai ne a kasar nan an rufe shi a shekarar 2014 biyowa bayan wata zanga zanga da ma’aikatan kamfanin suka yi akan rashin yanayin aiki mai kyau da ya sa ma’aikatan kamfanin suka susuce da kuma  jefa kamfanin cikin dimbin bashi.

Hukumar kamfanin da yan kasar waje ke jagoranta ta kori daukacin ma’aikatan kamfanin yan nijeriya daga tsarin ma’aikatan ta.

Fayemi ya shedawa manema labarai dake fadar shugaban kasa cewar ganawar da yayi da Buhari nada manufar sheda masa irin namijin kokarin da ake yi na dawowa da ayukkan kamfunnan gadam gadam.

Vision FM 92.1 Abuja

Theme Colors

Please select the following colors to preview different color schemes of the theme.