Languages

Gwamnatin jahar sokoto tace bazatayi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta samar da dukkan tallafin day a wajaba ga mata

Gwamnatin jahar sokoto tace bazatayi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta samar da dukkan tallafin day a wajaba ga mata , yara da kuma wasu jinsin al’umma masu bukata ta musamman a cikin jahar nan.

Anyi wannan jawabin ne a wurin bukin bude taron tattaunawa na kasa gameda lamurran mata da kuma cigaban al’umma karo  na goma sha bakwai da aka gudanar a yau.

A lokacin da yake jawabi, gwamnan jahar sokoto Aminu Waziri Tambuwal wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jaha farfesa Bashir Garba yace gwamnati ta samar da wata dama da za’a iya bada shawarwarin da zasu taimaka wajen samar da cigaba a jahar.

Ministar lamurran mata  Aishatu Jummai Alhassan tayi kira ga gwamnatin da ta cigaba da yin yekuwa akan barin yiwa yaya mata  aure tun suna kanana, kaciyar mata da dai sauransu.

Hakama mimistar ta godema gwamnatin jahar sokoto akan karamcin da kuma goyon bayan da aka nuna domin ganin cewa an gudanar da wannan taron wanda manufarsa itace samar da shawarwari masu amfani , da kuma samar da kafofin bunkasa zaman Lafiya

daga bisani ma’aikatar mata ta tarayya ta karrama gwamnan jihar sokoto akan kokari da kuma goyon bayan da yake baiwa mata da kuma kananan yara.

Vision FM 92.1 Sokoto

Theme Colors

Please select the following colors to preview different color schemes of the theme.