Languages

Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar saka dokar ba Aiki ba Albashi a matsayin wata hanya

Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar saka dokar ba Aiki ba Albashi a matsayin wata hanya ta mayar da martaba acikin sha’anin aikin gwamnati a Najeriya.

Ministan kwadago da ayyukan yi Chris Ngige ya bayyana wannan matsayar da aka cimma zuwa ga manema labarai dake fadar gwamnatin a karshen taron majalisar zartaswa ta tarayya da aka gudanar a Abuja.

Ngige yace tsayarwa da kuma aiwatar da wannan shawarar da majalisar zartaswa ta tarayya tayi, ya biyo bayan amincewar da majalisar tayi na shawarar da kwamitin kwararri akan harkar aikin gwamnati a matakin tarayya

An kaddamar da Kwamitin wanda ya samu jagoranchin sakataren gwamnatin tarayya da kuma shugaban ma’aikata a ranar 26 ga watan Afrilun shekara ta 2016

A yayinda yake ma manema labarai bayani akan abinda aka tattauna a wajen taron na majalisar zartaswa , ministan Lafiya farfesa Isaac Adewole yace gwamnatin tarayya nan bada jimawa ba zata hana  jami’an Lafiya yin wasu ayyuka a wajen wurarensu na aiki a fadin kasar nan.

A cewar ministan, doka bata baiwa duk wani jami’in gwamnati damar yin kowane aiki ba  face noma

Yace tuni an samar da kwamitin da zai baiwa gwamnati shawarar da ta dace akan lamarin.

Vision FM 92.1 Abuja

Theme Colors

Please select the following colors to preview different color schemes of the theme.