Languages

Cibiyar kare yaduwar curutoci ta kasa ta sanar da cewa ansamu sabuwar barkewar cutar kendar birai

Cibiyar kare yaduwar curutoci ta kasa ta sanar da cewa ansamu sabuwar barkewar cutar kendar birai akasar nan.

Wannan na kunshene acikin wani bayani mai dauke da sa hannun sakataren zartaswa na cibiyar Dr.Chikwe Ihekweazu. 

Yace ansamu Karin sabbin bullar cutar har guda 19 aduk fadin kasar nan bayaga goma sha biyu da akasamu ajahar Bayelsa.

Bayanin yakara da cewa sauran jahohin da akasamu bullar cutar sun hada da jahar Rivers da Ekiti da Akwa Ibom da Lagos dakuma Ogun kazalika da jahar Cross River.

Bayanga samun Barkewar cutar kendar Biri 22 ga watan Satumba 2017 ajahar Bayelsa sauran cutukan da akasamu asauran jahohi shidda wanda yakkawo jimillar cutukkan 31 ajahohi bakwai na  kasar nan.

Ihekweazu yace andauki nau’in kowace cutar domin yin gwaji adakin binciken cutukka tareda tabbatarwa.

Yace ma’aikatar Lafiya ta kasa ta hanyar cibiyar kare yaduwar curutukka tana goyon bayan jahohin da lamarin yashafa don ganin cutar bataci gaba da yaduwa bad a manufar takaita matsalar. 

Vision FM 92.1 Abuja

Theme Colors

Please select the following colors to preview different color schemes of the theme.