Languages

Majalisar dattawan Nijeriya tayi Allah wadai da yadda matasa ke cigaba da kwankwadar maganin tari

Majalisar dattawan Nijeriya tayi Allah wadai da yadda matasa ke cigaba da kwankwadar maganin tari watau kodin domin gusar da hankali inda majalisar dattawan tayyi kiran daukar matakan gaugawa domin magance matsalar don  cigaban matasa dama al’umma.

Wannan ya biyo bayan amincewa da wani kuduri akan batun da  Sanator Baba Garbai ya gabatar a zauren majalisar.

da yake gabatar da kudurin  Garbai yace kwankwadar miyagun kwayoyi musamman ganyen wiwi  da hodar iblis dadaddar matsala ce dake cigaba da yaduwa a tsakanin matasa maza da mata a jihohin arewacin kasar.

Ya kara da cewar yanzu haka ana samu rahotannin cewar yan matan dake karatu a manyan makarantun kasar nan na fuskantar kwankwadar maganin mura watau kodin.

A nasa kalamai dangane da kudurin  Senator Ben Bruce yace yana da kyau a daidai ta tattalin arziki domin samarwa matasa ayukkan yi da zai hana musu tsunduma cikin miyagun dabi’u.

Vision FM 92.1 Abuja

Theme Colors

Please select the following colors to preview different color schemes of the theme.