Languages

Hukumar zabe mai zaman kanta takasa ta nanata kudurinta na gudanar da zabe acikin gaskiya

Hukumar zabe mai zaman kanta takasa ta nanata kudurinta na gudanar da zabe acikin gaskiya da adalci wajen zaben cike gurbi na dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kware da Wamakko ajahar nan.

Kwamishinan zabe na jahar nan Ibrahim Jibrin Zarewa ya bayyana haka alokacin taron masu hannu ga lamarin wanda akayi a nan sokoto.

Ga abun da Kwamishinan ke cewa akan makasudin taron.

Kwamishinan yace za’ayi amfani da na’urar tantance katin zabe alokacin zaben cike gurbin.

Haka kuma wadanda sukeda katin wuccin gadi bazasu samu jefa kuri’aba da ayake na;urar bata iya ganin katin su.

Daya ke jawabi awurin taron kwamishinan yan sanda na jaha Ibrahim Idris yagar gadi magoya bayan yan siyasa dasu kaucema yin badai daiba alokacin yekuwar nemana zabe.

Ya yikira ga jam’iyyun siyasa  kada subari matasa suyi amfani da makamai dayake za’a kame duk wanda aka kama kuma za’a gurfanarda shi agaban kotu. 

Daga nan sai kwamishinan yan sandan ya bada tabbacin kudurin rundunar na ganin cewa anyi zaben hidda gwani cikin adalci amazabar.Taron dai yasamu halartar hukumomin tsaro da shugabannin addini.

Vision FM 92.1 Sokoto

Theme Colors

Please select the following colors to preview different color schemes of the theme.