Languages

Shugaban riko na jam’iyar PDP Ahmed Makarfi, ya sake nanata kudurin jam’iyar wajen mutun

Shugaban riko na jam’iyar PDP  Ahmed Makarfi, ya sake nanata kudurin jam’iyar wajen mutun tsarin nan na karba karba.

Makarfi, ya bayyana haka ne a Abuja yayin wani taro da shuwagabannin arewa da kuma dattawan jam’iyar PDP domin duba tsarin karba karba domin tunkarar zaben gama gari na shekara ta 2019 da kuma batun gudanar da babban taron jam’iyar na kasa da za’a gudanar a watan December.

Makarfi ya bukaci yayan jam’iyar akan su mutunta wannan tsari inda yace yana daga cikin matsayar da aka cimma a babban taron jam’iyar da aka gudanar a watan mayu a Birnin fatakwal.

Yace yana da kyau a tafi tareda kowa da kowa ta yadda wani ba zai ji an keta masa yancin da yake dashi ba wajen gudanar da wani tsari na jam’iyar.

Vision FM 92.1 Abuja

Theme Colors

Please select the following colors to preview different color schemes of the theme.