;
Breaking
An kashe mutum 21 a kudancin Kaduna

An kashe mutum 21 a kudancin Kaduna

Rahotanni daga kudancin jihar Kaduna na cewa mutane kusan 21 ne aka kashe a karamar hukumar Zangon Kataf a tashin hankali na baya-bayannan a yankin.

Kashe-kashen na zuwa ne kwanaki kadan bayan hukumomi a Najeriya sun ce sun tura karin jami’an tsaro a yankin domin kawo karshen zubar da jini.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da afkuwar lamarin, inda kakakinta, ASP Mohammed Jalige ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa mutum 21 ne suka mutu a yayin da uku suka samu raunuka.

Rahotanni sun ce an kaddamar da hare-haren ne a wasu kauyuka hudu na karamar hukumar Zangon Kataf a daren ranar Laraba.

Sai dai al’ummar yankin na cewa mutum 33 ne suka mutu cikin hadda kananan yara ba 21 kamar yadda ‘yan sanda suka sanar.