;
Breaking
Cacar Baki Ta Kaure Tsakinin Gwamna Nasiru El'rufai Da Majalisar  Dinkin Kan Hukuncin Dandaka Ga Masu Fyade

Cacar Baki Ta Kaure Tsakinin Gwamna Nasiru El'rufai Da Majalisar Dinkin Kan Hukuncin Dandaka Ga Masu Fyade

By Sulfidone

Gwamnatin Kaduna a Najeriya ta mayar da martani kan sukar da Majalisai Ɗinkin Duniya ta yi mata game da sanya hannu kan dokar yi wa masu fyaɗe dandaƙa.

A makon nan ne babbar jami'ar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce bai dace gwamnatin Kaduna ta dandaƙe mutanen da aka samu da laifin fyaɗe ba.

Babbar jami'ar, Michelle Bachelet, ta ce dandaƙe masu fyade tamkar an ɓata goma ɗaya ba ta gyaru ba.

Ms Bachelet ta ce: "Tsananta hukunci ba ya hana aikata laifi, a madadin haka kamata ya yi a tsorata masu aikata laifin ne da barazanar wasu hukuncin marasa tsauri, amma wanda suka tabbatar za a aiwatar da shi a kansu ba makawa."

Sai dai gwamnatin ta ce ƙazancewar da lamarin fyaɗe ya yi a jihar ce ta sanya ta ɗaukar tsattsauran hukunci.

Dokar da jihar Kaduna ta kafa kwanan baya ta samar da hukuncin dandaƙa ga duk wanda ya yi wa yarinya ko yaro mai shekara kasa da 14 fyade, kuma za a iya yanke masa hukuncin kisa.

Mata ma da suka aikata laifin za su fuskanci hukuncin cire mahaifarsu da kuma kisa.

Kwamishiniyar Shari'a ta jihar Kaduna Aisha Dikko ta ce lamarin fyaɗe a jihar ya zame wa jama'a wata ja'iba da ke buƙatar hukunci mai tsauri kamar dandaƙa.

"Kowace ƙasa da kowace al'umma akwai lamarin da ke damunsu, saboda haka muka yi dokar da za ta kawo wa mutanenmu sauƙin matsalolin da ke damunsu."

Ta ce jihar Kaduna ta dauki matakin ne domin magance matsalar kamar yadda aka yi a Bangladesh da wasu ƙasashen duniya.

Kwamishiniyar ta kuma ce, "Mu muna ganin tsananta hukunci kan masu fyaɗe zai kawo sauƙi."

Ta kuma bayyana cewa ganowa da hukunta masu aikata fyaɗe yana da wahala ba ma a Kadunan ba, har da sauran sassan duniya, "saboda wadanda aka yi wa fyaɗen na fargabar za a kyamace su."

"Yadda abin ya zama mana kamar annoba, shi yasa muka ga idan muka dauki wannan matakin, zai kai mu ga samin sauki kan al'amarin.

A 'yan watannin da suka gabata an rika samun rahotanni masu yawa da ke manuniya ga rashin daukar wani matakin da ya dace kan masu aikata laifukan fyade a Najeriya.