;
Breaking
Ɗalibai a Najeriya Sun Soma Jarrabawar Kammala Sakandare

Ɗalibai a Najeriya Sun Soma Jarrabawar Kammala Sakandare

A yau Litinin ɗaliban ajin ƙarshe na sakandare a faɗin Najeriya ke soma rubuta jarrabawarsu ta kammala karatu bayan da aka samu jinkiri na watanni saboda annobar cutar korona.

Ɗalibai fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar ne ake sa ran za su ɗauki tsawon makwanni suna rubuta jarrabawar da ake kira WAEC wadda kuma a kan yi a wasu ƙasashen yammacin Afirka.

Kusan mako biyu kenan da ɗaliban da ke shirin rubuta wannan jarrabawa suka koma makaranta domin sake kimtsa kansu.

Cutar korona ce ta haifar da tsaikon soma rubuta jarabawa sakamakon rufe makarantu tun daga watan Maris zuwa Yuli.Masu makarantu sun alƙawarta shirya jarrabawar bisa dokokin da aka tanadar don yaƙi da cutar korona, da suka haɗa da bai wa juna tazara a ɗakunan zana jarrabawar.

Nasara a jarrabawar WAEC ce ke tabbatar da kammala sakandaren ɗalibi da ba shi damar shiga jami’a da makarantun gaba da sakandare.

Najeriya ce dai ƙasar da ta fi yawan dalibai da ke rubuta wannan jarrabawar a makarantu sama da dubu 19 a da ke faɗin kasar.

Har yanzu dai jami’o'i da makarantun gaba da sakandare na ci gaba da kasancewa rufe a kasar.

Ministan ilimi a Najeriya, Chukwuemaka Nwajiuba ya ce mahukunta za su tabbatar ɗalibai komai ya tafi musu daidai har zuwa jami’a.