;
Daruruwan yan Nijar sun shiga zanga zangar lumana a birnin Yammai domin bukatar janyewar dakarun Faransa dake yaki da 'yan ta’adda da ake kira Barkhane daga kasar

Daruruwan yan Nijar sun shiga zanga zangar lumana a birnin Yammai domin bukatar janyewar dakarun Faransa dake yaki da 'yan ta’adda da ake kira Barkhane daga kasar

Daruruwan 'yan Nijar ne suka shiga zanga zangar lumana a birnin Yammai domin bukatar janyewar dakarun Faransa dake yaki da 'yan ta’adda da ake kira Barkhane daga kasar.

Masu zanga zangar sun yi ta shelar bayyana bukatar janyewar dakarun da kuma jinjinawa shugaban Rasha Vladimir Putin lokacin da suka yi tattaki zuwa gaban Majalisar dokokin kasar.

Rahotanni sun nuna cewar wasu daga cikin masu zanga zangar suna dauke da tutar kasar Rasha, tare da kuma rubuce rubucen dake sukar Faransa da Rundunar Barkhane.

Wasu daga cikin allunan na bayyana bukatar ficewar sojojin Faransar, yayin da suke bayyana cewar duk da zaman su a Nijar, ana ci gaba da kai hare hare ana kashe mutane.

Yace akwai akalla sojojin Faransa 3,000 a Yankin sahel, kuma wasu daga cikin su na Jamhuriyar Nijar, bayan janye su daga kasar Mali.

A watan Afrilun da ta gabata, 'yan majalisun Nijar sun kada kuri’ar amincewa da bukatar girke sojojin Faransa a kasar domin taimaka mata yaki da 'yan ta’adda.