;
El-Rufai ya kafa kwamitin bincike kan cin zarafin 'yan sanda a Kaduna

El-Rufai ya kafa kwamitin bincike kan cin zarafin 'yan sanda a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin shari'a da zai binciki cin zarafin da 'yan sanda suka aikata a jihar.

Wannan ya biyo bayan umarnin da Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa ta bayar na matakan da za a ɗauka domin yin gyara ga ayyukan 'yan sandan ƙasar kamar yadda masu zanga-zangar #EndSARS suka buƙata.

Cikin sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, mai taimaka wa Gwamna Nasir El-Rufai kan kafafen yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce za a rantsar da kwamitin da ƙarfe 11:00 na ranar yau Asabar.

Mambobin kwamitin sun haɗa da:

Mai Shari'a (mai ritaya) David Shiri Wyom - ShugabaAIG (mai ritaya) Lawal TankoRebecca Sako-John - Wakiliyar ƙungiyoyin farar hulaMustapha Jumare - Wakilin ƙungiyoyin farar hulaYakubu Umar Ibrahim - Wakilin ɗalibaiNathenial Sheyi Bagudu - Wakilin matasaInna Binta Audu - Wakiliyar Hukumar Kare Haƙƙi ta ƘasaHajara Abubakar - Wakiliyar Antoni Janar na Jihar Kaduna

Kaduna ta zama jiha ta huɗu da ta kafa kwamitin, wanda ake sa ran dukkanin jihohi za su kafa domin bincike da kuma biyan diyya ga waɗanda 'yan sanda suka ci wa zarafi a kowacce jiha a Najeriya.

Sauran jihohin da suka kafa kwamitocin sun haɗa da Legas da Filato da Ogun.