;
Breaking
FADAR SHUGABAN KASA TAYI NA'AM DA HUKUNCIN KOTUN BURTANIYA AKAN RIKICIN P&ID.

FADAR SHUGABAN KASA TAYI NA'AM DA HUKUNCIN KOTUN BURTANIYA AKAN RIKICIN P&ID.

Fadar Shugaban kasa tayi Na'am da Hukuncin kotun Burtaniya nayin da Bukatar Najeriya don na lokaci da Saukaka Hukuncin cin tarar kasar Dala Biliyan Goma ($10 billion), wanda kotun Da'ar Ma'aikata ta yanke kan rikici dake tsakanin kasar da Kamfanin (P&ID). Industrious Development Limited dake Najeriya.A Nazarin mu, Hukuncin yayi Dai de, zamu iya cewa ya Samar da wani dama mai karfi a rikicin Rashin Gaskiyar da aka tafka a Dillancin Iskar Gas tsakanin Najeriya da Kamfanin P&ID, dama hukuncin daya biyo baya da kotun ta yanke cewa Najeriya ta biya Dala Biliyan Goma ($10 billion). wanda kuma karara wani Yunkuri ne na Cutar da kasar biliyoyin Daloli da kamfanin da bai taba zuba jari a kasar mu ba.Bisa ga yarjejeniyar da aka yi, haka wani babbar dama ce nayin na'am da kotun na Burtaniya da Sauran su, da suka yanke Hukunci:"Najeriya ta taka wani Babban mataki don Tunkarar rikicin kan ikirarin kasar na cewa ita kanta Kamfanin dake Samar da Iskar Gas, (Gas Supply and Processing (GSPA). An kafane ta hanyar Cin hanci da Rashawa da aka biya wasu dai-dai ku, cikin wani bangare na Babban Shirin da aka shirya na Damfarar Najeriya." Sa'annan kuma akwai wani babban hasken nasara a Shari'ar tunda Babban Shaida na kamfanin (P&ID). Mr Quinn, ya bada Shaidar Karya ga Kotun, da kuma bada Sabanin Shaida wanda ke nuna shi kanshi Kamfanin (P&ID) bashi da ikon tafiyar da kwangilar da yake Ikirarin yi a kasar."Fadar Shugaban kasa ta Nuna jindadin ta, kan yadda Shara'ar ke tafiyar wanda ya haifar da wannan hukunci a kotun na Kasar Burtaniya, Fadar ta Shaida cewa hukuncin ya bada wani Dama da Saukaka wa Gwamnatin Najeriya kara bada kariya ga Kadarorin kasar daga Bata garin Kamfanoni da dai-dai kun Mutane.Dubi da wannan Hukuncin kotun na Burtaniya, haka ya Samar da yalwataccen dama ga Gwamnatin Tarayya taci gaba da kalubalantar Damfara da kamfanin ta shirya dama ture Hukuncin kotun na farko.A sabo da haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yaba wa Tawagar Lauyoyin da suka Wakilci Najeriya akan Rikicin da Kamfanin (P&ID), dama kara bada tabbacin ga 'yan kasa na Gari da Sauran kasashen Duniya akan Rashin Tararrabin Jajircewar sa na Yaki da Rashawa da cin Hanci ta kowani fuska.Mal. Garba Shehu: