;
Fadar shugaban Nijeriya ta mayar da martani a kan ikirarin da gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom yayi

Fadar shugaban Nijeriya ta mayar da martani a kan ikirarin da gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom yayi

Fadar shugaban Nijeriya ta mayar da martani a kan ikirarin da gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom ya yi cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya hana a dauki mataki kan Fulani makiyaya da ake zargi da tayar da hankali a jiharsa.

Kakakin Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana kalaman gwamnan a matsayin maganar da ba ta da tushe ballantana makama.

Ya kuma kalubanci Gwamna Ortom da ya bayyana sunayen jami'an tsaron da suka fada masa haka.

Fadar Shugaban kasa ta ce a halin yanzu kasar tana fama da matsalar tashe-tashen hankula, don haka bai kamata ‘yan siyasa su yi amfani da wannan dama ba wajen kawo baraka tsakanin al'umomin kasar.