;
Femi Fani Kayode ya tuba bayan ya sha suka daga 'yan Najeriya

Femi Fani Kayode ya tuba bayan ya sha suka daga 'yan Najeriya

Ƙurar da ta tashi bayan tsohon ministan zirga-zirgar jiragen saman Najeriya Femi Fani Kayode ya ci mutuncin wani ɗan jaridar Daily Trust a Najeriya ta tilasta masa bayar da hakuri.

Ranar Talata ne wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna tsohon ministan yana zagin ɗan jaridar, Eyo Charles, bayan ya yi masa wata tambaya yayin wata hira da 'yan jarida.

Hasalima Mista Fani Kayode ya yi wa ɗan jaridar barazanar daukar mataki a kansa.

Eyo Charles ya tambayi Mista Kayode cewa "wane ne yake ɗaukar nauyin rangadin da kake yi a jihohin Najeriya inda kake duba ayyukan da gwamnoni ke yi?"

Tambayar ta ɓata ran tsohon minstan, inda ya rika zagin dan jaridar.

Hakan ya janyo masa suka daga bangarori da dama, ciki har da jaridar Daily Trust da kungiyar 'yan jarida ta Najeriya da kuma ƙungiyar kare hakkin ɗan Adam ta Amnesty International.

Sai dai a wani saƙo da Mista Kayode ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba, ya ce ya janye kalaman da ya furta kan ɗan jaridar.

A cewarsa: "Ina da abokai da yawa 'yan jarida waɗanda na ɓata wa rai bayan na harzuƙa da na yi amfani da zafafan kalamai. Na janye waɗannan kalaman da na yi amfani da su."

Ya kuma bayyana cewa bai taɓa lafiyar jikin ɗan jaridar ba kuma bai tura kowa ya yi masa barazana ba. "Duk wanda ya ce na yi wani abu na daban ya kawo shaida."

"Fiye da shekaru 30 da suka wuce, na yi aiki tare da kare 'yan jarida da kuma gwagwarmayar tabbatar da 'yanci tare da su. Ina da abokai saosai 'yan jarida," in ji shi.

A ranar Talata dai Mista Kayode ya fito fili ya bayyana cewa ba zai bayar da haƙuri kan irin cin mutuncin da ya yi wa ɗan jaridar ba, sai dai fitowar da ya yi yanzu ya bayar da hakuri, ba ya rasa nasaba da irin wutar da ƙungiyoyi da wasu fitattun mutane suka hura wa Mista Kayode musamman a shafukan sada zumunta.