
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewar soke jami’an yan sanda na musamman na rundunar SARS da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da babban sufeton yan sanda babban abun yabawa ne
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewar soke jami’an yan sanda na musamman na rundunar SARS da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da babban sufeton yan sanda babban abun yabawa ne, sai dai ya bayyana cewar akwai fargabar kar yin hakan ya haifar da samun wasu gungun yan ta’adda a kasar nan.
Haka ma gwamnan yace kamata ya yi ace babban sufeton yan sanda ya tun-tubi al’ummar kasar nan akan hanyoyin da za’a bi domin inganta ayukkan yan sanda ta yadda za su rika gudanar da ayukkanasu dai-dai da muradun al’ummar kasar nan.
Ya kara da cewar sauya sunan jami’an yan sanda na musamman daga SARS zuwa rundunar yan sanda ta SWAT ba zai magance matsalolin da kasar nan ke fuskanta ba.
Saboda haka gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da shawara ga shugaban kasa daya sake daukar sababbbin jami’an tsaro tare da samar musu da ingantattun kayan aiki na zamani da kuma inganta jin dadin jami’an na tsaro.
Da yake magantawa akan sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jaha da mambobinsa da aka rantsar, gwamnan yace an zabe sune a bisa can-cantar da suke da ita da kuma gaskiya da rikon amanar da suke da shi a ya yin da suke gudanar da ayukkan su a lokacin da suke aikin gwamnati.
Haka ma gwamna Tambuwal ya bukaci hukumar ta zabe data fito da wasu tsare-tsare da fitar da jadawalin yadda za’a gudanar da zaben, ta yadda hakan zai bai wa gwamnati damar bayyana lokacin da ya kamata a gudanar da zaben nan bada dadewa ba.
A ya yin rantsuwar dai gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya taya su murnar samun wannan mukaman, inda kuma ya yi kira gare su da su gudanar da aikinsu kamar yadda ya dace ba tare da nuna nwani ban-banci ba a ya yin gudanar da aikin nasu.
Sababbin shugabannin hukumar ta zabe mai zaman kanta ta jaha sun hada da Aliyu Suleiman a matsayin shugaba da mambobinsa guda biyar da suka da Mu’azu Garba Dundaye da Sidi Muhktar Ibrahim da Umar Galadima Durbawa sai Abubakar Halliru Dange da kuma Alhaji Musa Illela wadanda dukkaninsu suke a zaman mambobin hukumar na din-din-din!