;
Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya kamu da Cutar Korona.

Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya kamu da Cutar Korona.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya kamu da Cutar Korona.

Mista Fayemi ya bayyana hakan ne a safiyar jiya Laraba a shafinsa na Twitter, in da ya ke cewa “Na yi gwajin cutar korona, kuma an tabbatar min da cewa na kamu.

“A yanzu ina lafiya kuma na bukaci da a kekance ni cikin gida na, in da zan samu kulawa daga kwararrun likitoci na. Na daura mataimaki na a matsayin wanda zai ci gaba da gudanar da harkokin gwamanati, amma zan ci gaba da aiki na na yau da kullun daga gida,” gwamnan ya rubuta a Tiwita.

Mista Fayemi ya shiga cikin jerin gwamnonin jihohi da sauran manyan ‘yan Nijeriya wadanda su ka kamu da cutar, kamar gwamnan Jihar Kaduna, Oyo, Bauchi da Delta, wadanda kuma da yawa daga cikinsu duk sun warke daga cutar.