;
Gwamnan Jihar Kaduna Ya Amince Da Yin Sallar Idin Babbar Sallah

Gwamnan Jihar Kaduna Ya Amince Da Yin Sallar Idin Babbar Sallah

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya amince da yin sallar Idin babbar sallah a fadin jihar amma a fili ba cikin masallatai ba. Gwamnan ya jaddada cewa babu shagalin bikin salla bayan sallar idin.Gwamman ya amsa wasu tambayoyin da akai masa kamar hakaTambaya:Gwamnatin Tarayya ta sanya ka’idoji na bude makarantu har wasu jihohin sun fara shirye-shirye. Shin Jihar Kaduna ta fara shirin bude makarantu?Amsa:Fannin ilimi wani fanni ne da kowace jiha take da ikon gashin kanta a kai kuma Kaduna za ta yi nata irin tsarin na ganin ta kare rayuwar ‘ya’yanta. Amma akwai abubuwan da muka yi tarayya da sauran jihohi da kuma Gwamnatin Tarayya kamar sha’anin abin da ya shafi jarrabawar WAEC. Ma’aikatarmu ta ilimi na nan na tsare tsare su bude makarantu in lokacin jarrabawar ya yi. Na san makarantu masu zaman kansu sun kosa a bude makarantu, amma wani abu ne da ake ta muhawara a matakin Tarayya da jihohi kan wane lokaci ya fi dacewa da a bude makarantu ba tare da yaronmu sun kamu da cutar Korona ba. Ku kanku sheda ne a tsaye muke game da wannan lamarin.

Tambaya:An bude masallatai saboda sallar Juma’a da kuma majami’u saboda ibadu ranar Lahadi sai dai har yanzu ba a bude masallatai saboda salloli biyar da kuma majami’u na ibadun cikin mako. Yaushe ake sa ran bude wadannan wuraren?Amsa:Shugabannin addinai suna kokari matuka wurin ganin an kiyaye matakan da aka sa na yaki da cutar Korona Bairos sai dai masu bin umurnin nan ba su wuce kashi 75%. Wasu wuraren ma ba a kai kashi 40% ba. Saboda haka muna kara rokon shugaban al’umma su ci gaba da wayar da kan al’umma.Masana kiwon lafiya sun ba mu shawara mu kara dan dakatawa kafin mu bar al’umma su koma wuraren ibadu gaba daya

Tambaya:A lokacin da aka sassauta wannan doka ta kulle, ka ba alummar Jihar Kaduna shawara cewa yanzu yaki da wannan cuta ta Korona Bairos ta dawo hannunsa kowa ta dauki matakin kare kansa. Shin ka gamsu da yadda al’ummar Jihar Kaduna ke bin dokokin da ka sanya na kare kai daga kamuwa da covid-19?Amsa:Kamar yadda na fada muku a baya muna fuskantar matsaloli na yadda al’umma ke bin matakan kariya daga kamuwa daga Korona Bairos. Mutane kamar sun dauka tunda an cire dokar kulle an gama maganar Korona Bairos ne ta wuce. Mutane sun bar sanya takunkuminsu , sun bar bayar da tazara. Wannan ba lokacin da ya kamata mu yi sakaci ba ne. bincike ya nuna cewa duk wanda ya kamu da wannan cuta takan bar masa wani lahani a jikinsa ko da kuwa ya warke.Mun kaddamar da wani salo na yaki da cutar Korona da muka kira “Forward Campaign” a watan Yuni. Wannan wani salon yaki ne da cutar ta yadda kowa zai dauki matakin kare kansa. Duk wanda ya damu da lafiya da rayuwarsa da na iyalansa da na ‘yan uwansa da na makwaftansa zai rungumi wannan kamfe da muka fara na “Ci Gaba Da Yaki Da Korona Bairos” ta hanyar:• Sanya takunkimi• Bayar da tazara• Tsafatan kafofin numfashi• Wanke hannaye akai akai• Kaurace wa tarurruka• Zama a gida da kuma• Cin abinci masu kara garkuwan jikiIna rokon kowa da kowa ya yi iya kokarinsa domin kare kansa da kuma sauran al’umma ta hanyar bin matakan kariya daga kamuwa da Covid-19. Ina rokon al’umma mu yi duk abin da za mu yi domin ganin bayan Korona Bairos.Mun kara yawan wurin jinya a jihar, mun sanya kayan aiki da ma’aikata. Muna gina sabon wurin jinya na cututtuka masu yaduwa mai gado 136, sannan muna kokarin ganin mun samar da dakunan jinya masu gado 20 ko 30 a kowane babban asibiti da ke jihar. Mun kara wuraren gwaji.Amma fa ya kamata mu sani duk da kara inganta fannin kiwon lafiyarmu, in muka yi sakaci cutar Korona Bairos ta ci gaba da yaduwa za a zo lokacin da zai fi karfin asibitocinmu da ma’aikatanmu. Ya kamata mu sa a ranmu cewa akwai wata bala’a’aiyar annoba tana yawo a kokarin da muke yi na ci gaba da gudanar da hanrkokinmu na yau da kullum. Saboda haka, mu ci gaba da daukan matakan kariya domin dakile yaduwar Korona Bairos.

Tambaya:Ranar 9 ga watan Yuni 2020, ka sanar da sake bude jihar bayan dokar kulle da aka a kokarin da gwamnatin ke yi na yaki da cutar Korona Bairos, aka bude wuraren kasuwanci da ma’aikatun gwamnati. Kimanin wata daya kenan da bude kaduna, wane hali ake ciki game da yaki da cutar Covid-19 a yanzu?Amsa:Zan fara da jinjina wa al’ummar Jihar Kaduna na irin goyon baya da jajircewan da suka yi na tsawon kwana 75 a kulle. Mun dauki wannan mataki domin dakile yaduwar kuma inganta fannin kiwon lafiyarmu ta yadda za mu iya gano masu wannan kuma mu ba su kulawar da ta dace.Kuma alhamdulillah kasuwanci da sauran harkoki na tattalin arziki sun fara farfadowa.Amma duk da haka mun fahimci akwai rashin bin dokokin da aka sa na kariya daga kamuwa daga cutar Korona Bairos tun lokacin da aka sassauta dokar.A safiyar yau 22 ga watan Yuni 2020, wadannan su ne alkaluman masu cutar Covid-19:• Mutanen da aka yi wa gwaji: 10,550. (An yi wa mutum 212,000 gwaji a Nijeriya)• Mutanen da suka kamu: 1211• Mutanen da aka sallama: 931• Mutanen da suke jinya: 206• Mutanen da suka mutu: 20

Tambaya:1. Maigirma Gwamna da farko dai zan fara da taya ka murna na labarin da ke yawo cewa Jihar Kaduna ta zama jiha wanda ta fi kowace jiha janyo ra’ayin masu zuba jari daga kasashen waje, sannan a bara ma Babban Bankin Duniya ta ba Kaduna lambar yabo cewa ita ce jihar da ta fi kowace jiha dadin kasuwanci. Wane irin dabaru Kaduna ke yi na da ke na janyo hankulan irin wadannan masu lura da al’amurran?Amsa:Assalamu alaikum. Na gode maka amma wannan yabo ne ga ilahirin mutanen da muke aiki da suke kokarin ganin sun janyo ra’ayin masu zuba jari zuwa jiharmu da kuma ma’aikatunmu da suke aiki domin ganin sun saukaka kasuwanci a jihar. Duk gwamnatin da ta san abin da take yi ya kamata ta yi duk abin da ya dace wurin ganin ta janyo hankulan masu zuba jari ta hanyar yin tsare tsare da kudurorin domin taimakon al’umma da bunkasa kasuwanci da samar da aikin yi da kuma bunkasa tattalin arziki.Muna da yawan al’umma kimanin miliyan 10, wanda kashi 85% matasa ne kasa da shekara 35. Hakkinmu ne mu samar wa wadannan matasan ayyukan yi. Gaba daya ma’aikatan da ke aiki da Gwamnatin Jihar Kaduna ba su wuce mutum 100,000 ba. Saboda haka hikimar da za mu yi ita ce kawai mu janyo kamfanoni masu zaman kansu domin samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki.

Tambaya:Gwamnatin Tarayya ta sanya ka’idoji na bude makarantu har wasu jihohin sun fara shirye-shirye. Shin Jihar Kaduna ta fara shirin bude makarantu?Amsa:Fannin ilimi wani fanni ne da kowace jiha take da ikon gashin kanta a kai kuma Kaduna za ta yi nata irin tsarin na ganin ta kare rayuwar ‘ya’yanta. Amma akwai abubuwan da muka yi tarayya da sauran jihohi da kuma Gwamnatin Tarayya kamar sha’anin abin da ya shafi jarrabawar WAEC. Ma’aikatarmu ta ilimi na nan na tsare tsare su bude makarantu in lokacin jarrabawar ya yi. Na san makarantu masu zaman kansu sun kosa a bude makarantu, amma wani abu ne da ake ta muhawara a matakin Tarayya da jihohi kan wane lokaci ya fi dacewa da a bude makarantu ba tare da yaronmu sun kamu da cutar Korona ba. Ku kanku sheda ne a tsaye muke game da wannan lamarin.