;
Breaking
Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Sassuta Dokar Hana Fita A Kananan Hukumomin Zangon Kataf Da Kauru

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Sassuta Dokar Hana Fita A Kananan Hukumomin Zangon Kataf Da Kauru

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassuta dokar hana fita a ƙananan hukumomin Zangon Kataf da Kauru da ke fama da rikicen-rikicen ƙabilanci da na addini.

Sanarwar da Kwamishinan Tsaron Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar a yau Asabar ta bayyana cewa daga yanzu dokar za ta riƙa aiki ne daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.

“Yayin da muke ƙoƙarin daƙile salwantar rayukan al’umma da tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’ummomin Atyap da Fulani da Hausawa, Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da shawarar sassauta dokar hana fita,” in ji sanarwar.

“Daga yau (Asabar) dokar za ta riƙa aiki daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a Zangon kataf da Kauru.”

Tun a ranar 11 ga watan Yunin 2020 aka saka dokar hana fita ba dare ba rana bayan wani rikicin ƙabilanci tsakanin Hausawa da ‘yan ƙabilar Atyap kan wata gona.