;
Gwamnatin Jihar Kaduna  Tace  Dalibai Ba Za Su Koma Karatu Ba

Gwamnatin Jihar Kaduna Tace Dalibai Ba Za Su Koma Karatu Ba

A daidai lokacin da ake shirin bude makarantu a fadin Najeriya, bayan da gwamnatin tarrayar kasar ta ce za a iya komawa karatu daga ranar 18 ga watan Junairu – wasu jihohin kasar sun ce kada a bude makarantu saboda cutar korona.

A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, gwamnatin jihar ta ce ba ta saka ranar komawar dalibai ba kuma dukkan makarantu za su kasance a rufe har sai abin da hali ya yi.

Babban sakatare a ma’aikatar ilimin jihar, Phoebe Sukai ya ce gwamnati na nazarin batun kafin yanke shawarar ranar bude makarantu a fadin jihar Kaduna.

A cewar hukumomi a jihar, har sai gwamnati ta kammala daukar matakan da suka dace kafin bude makarantu.