
Gwamnatin jihar Kano ta haramta sana'ar adaidaita sahu daga karfe goman dare a fadin jiharr
Gwamanatin Kano ta ce daga ranar Alhamis 20 ga Yulin da muke ciki ta harmata sana’ar adai-daita sahu bayan karfe na10:00 dare a fadin jihar nan.Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammadu Garba ya fitar ranar Litinin.
Ya ce an cimma matsayar ne a taron masu ruwa da tsaki kan al’amurna tsaro a jihar nan.
Garaba ya kara da cewa matakin wani bangare ne na ganin an kare lafiya da dukiyoyin al’umma a fadin jihar Kano.
Ya kuma bukaci masu sana’ar a daidaita sahu su bada hadin kai kan wanana doka, a cewarsa jami’an tsaro za su hukunta duk wanda aka kama ya karya dokar.