;
Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin kara mafi karancin albashin ma'aikata daga N30,000 da ake biyan  a halin yanzu.

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin kara mafi karancin albashin ma'aikata daga N30,000 da ake biyan a halin yanzu.

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin kara mafi karancin albashin ma’aikata daga N30,000 da ake biyan ma’aikata a halin yanzu.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ne ya bayyana haka a Abuja yayin da yake jawabi ga mambobin kungiyar kwadago ta kasa NLC a wajen wani taron baje kolin wata takarda mai suna, “Tarihin Zamani na Gwagwarmaya Aiki.

Ngige ya bayyana cewa karin albashi mafi karanci ya zama dole saboda hauhawar farashin kayayyaki a duniya da ya yi tasiri ga karfin saye da ‘yan kasa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a 2019, ya sanya hannu kan dokar mafi karancin albashi. Sai dai Jihohi da dama, a cewar shugabannin kwadago, har yanzu ba su aiwatar da dokar biyan ma’aikatansu Naira 30,000 ba.
Hafizu usman dabire

Gaskiya wannan starin yayi muna fatar abin zai dore