;
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya, ta yi gargadin yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a wasu jihohin kasar 14 sakamakon tumbatsar kogunan Niger da Benue.

Gargadin wanda NEMA ta fitar da hadin gwiwar hukumar da ke kula da koguna ta kasar sun ce ambaliyar za ta shafi jihohin Adamawa da Taraba da Benue da Neja da Nassarawa da Kebbi da kuma Kogi da sauransu.

A jawabinsa gaban manema labarai, darakta janar na hukumar Mustapha Habib Ahmed ya bukaci gwamnatocin jihohin da ambaliyar za ta shafa su dauki matakan sauya matsugunan al’ummomin da ke cikin hadari don basu kariya daga ambaliyar.

Mustapha Habib Ahmed ya ce a zantawar da ya yi da hukumar kula da koguna ta Najeriya, sun tabbatar mishi cewa masu kula da madatsar ruwa ta Lagdo a Kamaru sun saki wani adadi na ruwa daga ma’adanarsu ranar 13 ga watan da muke ciki na Satumba, wanda kai tsaye ruwan zai shiga kogin Benue.

Hukumar kula da koguna ta Najeriya NIHSA ta bada tabbacin cewa shigowar ruwan daga Kamaru yanzu haka ya cika ma’adanan ruwan da kasar ke da su da suka kunshi Kainji Jebba da kuma Shiroro wadanda ake sa ran suma su tumbatsa daga yanzu zuwa karshen watan Oktoba mai zuwa.