;
Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da ke sintiri a kan babbar hanyar Okene zuwa Abuja, sun kama wata motar bas dauke da bindigogi guda 18 da harsashi 1,300 a jihar Kogi

Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da ke sintiri a kan babbar hanyar Okene zuwa Abuja, sun kama wata motar bas dauke da bindigogi guda 18 da harsashi 1,300 a jihar Kogi

Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da ke sintiri a kan babbar hanyar Okene zuwa Abuja, sun kama wata motar bas J-5 dauke da bindigogi guda 18 da harsashi 1,300 a jihar Kogi.

Motar ta fito ne daga Onitsha, jihar Anambra ta nufi hanyar Kaduna-zaria a jihar Kaduna.

Rahoton ya fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi.

Ya ce, “Hukumar ta kuma cafke wani Anthony Agada mai shekaru 37, dauke da harsashi 1,000 a cikin wata motar bas da ta taho daga Onitsha zuwa Abuja duk a rana daya.