;
Jami'an Tsaro Sun Kwashe Almajiran Dahiru Bauchi A Kaduna Cikin Dare

Jami'an Tsaro Sun Kwashe Almajiran Dahiru Bauchi A Kaduna Cikin Dare

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa gamayyar jami'an tsaro sun kutsa cikin gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda suka kwashe duka almajiran da ke kwance a tsakar gidan.

Shugaban makarantun Dahiru Bauchi na Kaduna da kewaye kuma limamin masallacin bye pass na Kaduna, Fatahu Umar Pandogari, ya tabbatar wa mane labarai  da faruwar wannan lamarin.

"Da misalin 12:00 na dare Sojoji da Ƴan sanda da Kastelea da Road Safety suka shigo gidan Maulanmu Shehu, nan makaranta, suka kama almajirai suka tafi da su cikin daren," in ji shugaban makarantar.

Ya bayyana cewa bai san dalilin da ya sa aka kama almajiran ba, amma tun bayan rufe makarantu lokacin ɓullar korona a karon farko, tun lokacin aka sallami ɗaliban makarantar, amma a cewarsa, waɗanda aka kama a yanzu waɗanda suke zaune a gidan Sheikh Dahiru ne ba wai waɗanda suka taso suka zo daga wani gari ba.

"Ba za mu iya tantance ko almajirai nawa aka ɗiba ba, domin cikin dare aka zo aka kwashe su," in ji shi.

Ya kuma bayyana mana cewa sun yi ƙoƙarin tuntuɓar gwamnatin Kaduna a lokacin da abin ya faru, amma ba su samu damar magana da su ba.

Amma ko da BBC ta tuntuɓi gwamnatin Kaduna, mai taimaka wa gwamnan Kaduna kan kafafen yaɗa labarai Abdallah Yunus Abdallah, ya shaida mana cewa a halin yanzu ba za su ce komai kan wannan lamari ba, amma nan gaba kaɗan za su fito su yi ƙarin bayani.

Babu wani tabbaci dai kan dalilin da ya sa aka kai wannan samamen, amma ko a kwanakin baya sai da gwamnatin jihar ta ƙwace lasisin wata makaranta da kuma rufe ta sakamakon zarginta da saɓa dokokin korona.
Mustapha

Allah kawo Mana zaman lafia ameen

USMAN YAHUZA

ALLA YAKAWO SAUKI