
Kimanin naira Miliya 12 muka kashe wajen tallafawa masu bukata ta musamman domin bikin Sallar Layya gwamnatin Kano
Zubin rubutu Saifullahi Gambo MinjibirKimanin naira miliya 11 da dubu dari uku da talatin, Gwamnatin Jihar Kano ta kashe wajen siyan kayan tallafin sallah ga masu bukata ta musamman da gidajen gajiyayyu.Kayayyakin da suka hada da Shanu Raguna, Shinkafa, Man girki da dai sauransu.Hajiya Ma'azatu Isah Dutse MNI ita ce babbar Sakatariya a ma'aikatar Ayuuka na musamman jan hankalin masu bukata ta musamman tayi kan cewa su yada wannan alkhairi da gwamnatin ta yi musu ga na kasa da su.Shi ma a nasa jawabin sakataran hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano Dr Sale Aliyu Jili yabawa gwamnatin jihar Kano yayi karkashin jagirancin Dr Abdullahi Umar Ganduje bisa wannan kikari da yayi.A karshe suma wadanda suka amfana da tallafin da suka hada da sarakunan masu bukata ta musamman da galadimominsu su mika godiyar su ga hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano karkashin jagirancin babban sakataran hukumar bayar da agajin gaggawa kwamared Dr Sale Aliyu Jili