;
Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai mai kula da harkokin ilimin bai-daya,  ya gargadi gwamnonin kasar nan da su ba da fifiko ga ilimin firamare.

Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai mai kula da harkokin ilimin bai-daya, ya gargadi gwamnonin kasar nan da su ba da fifiko ga ilimin firamare.

Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai mai kula da harkokin ilimin bai-daya, ya gargadi gwamnonin kasar nan da su ba da fifiko ga ilimin firamare ko kuma su kasance a shirye kan sakamakon da zai biyo baya.

Shugaban kwamitin Farfesa Julius Ihonvbere ne ya bayyana haka a Ilorin babban birnin jihar Kwara a karshen ziyarar kwanaki biyu da suka kai domin duba ayyukan Hukumar da aka kammala a jihar.

Ya ce ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta jihohin da aka samu sun karkatar da tallafin da hukumar kula da Ilimin bai-daya ke bai wa Jihohi ba.