;
Ma'aikatar Tsaron Rasha ta sanar da kisan sojojinta kusan dubu 6 a yakin da ta shafe tsawon watanni 7 ta na gwabzawa a Ukraine,

Ma'aikatar Tsaron Rasha ta sanar da kisan sojojinta kusan dubu 6 a yakin da ta shafe tsawon watanni 7 ta na gwabzawa a Ukraine,

Ma'aikatar Tsaron Rasha ta sanar da kisan sojojinta kusan dubu 6 a yakin da ta shafe tsawon watanni 7 ta na gwabzawa a Ukraine, wanda ke matsayin karon farko da Moscow ke fitar da jumullar alkaluman dakarun da ta yi asara a yakin.

Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu a wani jawabin kai tsaye da ya gabatar ta gidan talabijin ya ce dakarun kasar dubu 5 da 937 suka mutu a Ukraine tun bayan farowar yakin a watan Fabarairu zuwa yanzu, yakin da Moscow ke nanata cewa ta na yi ne don kare martabar al'ummarta.

Wannan sanarwa na zuwa a dai dai lokacin da shugaba Vladimir Putin ke bayyana wani sabon shirin daukar sabbin sojoji dubu 300 aiki a sassan Rasha, a wani yunkuri da kasashen Duniya ke ganin jagoran na Moscow na shirin karfafa dakarunsa don dorawa a yakin da ya ke a Ukraine, dai dai lokacin da yankin 'yan aware na Ukraine ke shirin kada kuri'ar ballewa daga kasar don hadewa da Rasha.

Tuni dai kasashen Duniya suka fara kakkausar suka ga matakin na Putin, inda kungiyar tarayyar Turai ke ganin yunkurin daukar sojojin dubu 300 ya nuna karara yadda Putin ya damu da rashin nasararsa a yakin na Ukraine, yayinda Jamus ta bayyana yunkurin a matsayin wani lamari da bazai haifarwa kasar da mai ido ba.