;
Mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar yayi kira ga shugabannin siyasa da su saka tsoron Allah ga shugabancin al’umma saboda dukkanin hakkokinsu sun rataya ne a wuyansu.

Mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar yayi kira ga shugabannin siyasa da su saka tsoron Allah ga shugabancin al’umma saboda dukkanin hakkokinsu sun rataya ne a wuyansu.

Anyi kira ga shugabannin siyasa da su saka tsoron Allah ga shugabancin al’umma saboda dukkanin hakkokinsu sun rataya ne a wuyansu.

Mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ne yayi wannan kiran a lokacinda ministar lamurran jinkan bil’adama Haj Sadiya Umarda takwarar ta ta lamurran mata Paulin Tallen suka kai masa ziyara a fadarsa.

Ministar lamurran jinkan bil’adama tazone jihar sakkwato domin bayar da kayan rage hassahi ga wadanda iftila’in ambaliya ya rutsa da su yayinda takwarar ta ta mata kuwa tazao jihar sakkwato domin cigaba da wayarda kan al’umma kan ilimin ‘ya’ya mata.

Mai alfarma sarkin musulmin ya yabawa ministocin biyu kan ziyarar da suka kawo yana mai cewar jihar sakkwato ta duki ilimin ‘ya’ya mata da muhimmanci.

Ya kuma bayyana tarihin ilimin mata ga diyar mujaddadi Sheikh Usmanu Bin Fodio nana Asma’u.

A jawabansu daban daban ministocin Sadiya Umar da Paulen Tallen, sun bayyana cewar sunje ne fadar domin domin neman albarka tare da gabatar da kayayyakin rage hassahin ga gwamnatin jihar sakkwato domin rarrabasu ga wadanda iftila’in ya rutsa da su.

Haka kuma zasu kaddamar da shirin tallafawa mata da kudi na gwamnatin tarayya.