;
Makon Danfodiyo; Margayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da sarkin Kano na 13 Ado Bayero na daga cikin wadanda suka karbi kambun Sheick Danfodiyo a Sokoto

Makon Danfodiyo; Margayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da sarkin Kano na 13 Ado Bayero na daga cikin wadanda suka karbi kambun Sheick Danfodiyo a Sokoto

Daga Aminu Alhussaini Amanawa a Sokoto.

Margayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da sarkin Kano na 13 Ado Bayero na daga cikin wadanda suka karbi kambun karramawa a makon Dan Fodio na bana da ya gudana a Sakkwato.

Sauran wadanda suka samu wannan kambun sun hadar da Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh da ya samu kambun karramawa na kani ga Dangodiyo Sheikh Abdullahi Fordioyo yayin da kambun Nana Asma’u mai taken cigaba ya fada hannun tsohon mataimakin gwamnan jihar Lagos Alhaja Lateefat.

Shi kuma Kambun mai alfarma sarkin musulmi ya fada hannun Madawakin Gwandu, Idris yayin da a dayan bangaren kambun wanzar da zaman lafiya na sarkin ya fada hannun Imam Fu’ad Adeyemi.

Da yake magantawa yayin gudanar da bikin, mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa wadanda suka samu karramawar sun same ta ne ta la’akari da irin gudunmawar da suka bayar, inda ma ya bada misali da irin gudunmawar da fitaccen malamin addinin musuluncin nan a Kaduna margayi Sheich Gumi dama Margayi sarkin Kano Ado Bayero suka bayar wajen cigaban al’ummar su dama kasa baki daya.Hakama sarkin ya bayyana bukatar dake akwai na samar da hadin kai a tsakaniin ‘yan kasa, da a cewar sa galibin wadanda aka karramar, sun bada gudunmawa sosai duk kuwa da cewa yankunan su basa karkashin Daular Usmaniya.

Da yake magantawa a madadin wadanda aka karramar, Da ga fitaccen malamin addinin musuluncinn Sheikh Ahmad Mahmoud Gumi yayi kira ga sarkin, ya bayyana bukatar dake akwai na samar da wani fage da manufar tattaunawa domin kawar da ban-bance- banbance.

Bukatar fassara littafan Daular Usmaniyya zuwa Harshen Hausa

Wanin shehin malamin jami’a farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya bayyana bukatar fassara littafan lissafi dana sauran kimiyya da fasaha zuwa harsunan gida.

A cewar shehin malamin fassarawar zai taimakawa dalibban Njaeriya musamman ma wadna suka a matakin farko na Primary da karamar sakandiri wajen fahimtar abubuwan da ake koya masu.Shehin malami Yadai yi wannan kiran ne sa’ilin gabatar da wata Makala mai taken amfani da harshen uwa wajen ilmantar da dalibai ilimin boko, ta amfani da salon malaman daular Usmaniya.Gabatar da makalar dai na zuwa ne daga cikin jerin bukukuwan makon Danfodiyo karo na 9 da kungiyar matasa musulmai ta kasa NACOMYO ke shirywa a duk shekara hadin guiwa da majalissar mai alfarma sarkin musulmi da kuma kungiyar dalibai ta kasa reshen jihar Sokoto.

A cewar shehin malamin yanzu lokaci yayi da yakamata a rika horas da dalibai da harsunan uwa inda ma ya bada misali harshen uwa da yayi amannar cewa hakan zai samar da sauyyi a cikin al’umma.

Professor Aliyu Muhammad Bunza hakama yayi amfani da wannan damar wajen kira ga majalisar mai alfarma sarkin musulmi data dabbakar da hakan, ta hanyar samar da wani kwamitin kwararru da zai yi aikin fassara littafan kimiyya zuwa harshen uwa.Shima wani kwararren shehin malami Dahiru Muhammad Argungu, sa’ilin da yake ta’aliki kan makalar kira yayi da a sake fasalin tsarin harsunan kasar nan.

Wazirin Sokoto, Professor Sambo Wali Junaidu wanda ya kasance babban bakon da ya jagoranci gabatar da makalar, ya bayyana muhimmancin dake tattare da amfani da harshen uwa wajen ilmantar da al’umma.Sauran wadanda suka maganta a wajen taron sun hadar da shugaban hukumar zakka da wakafi na jiha Muhammad Lawal Maidoki, kafafen yada labarai dama dalibai.

Gudunmawar Shehu Danfodiyo Da Mataimakansa

Masana sun yi amannar cewa gudunmawar da Shehu Usmanu Danfodiyo da sauran wadanda suka samar da daular Usmaniya suka bayar na cigaba da kasancewa fage na Da’awah ga ma wadanda ba musulmai ba.Shugaban kungiyar dalibai musulmi na kasa ( MSSN) Mal. Shehu Uthman Abubakar shine ya bayyana hakan lokacin gabatar da Makala mai taken Da’awah ga wadanda ba musulmai ba, dama gudunmawar su, a wajen bikin gabatar da makaloli da kungiyar matasa musulmai ta kasa NACOMYO reshen jihar nan ta Sokoto suka shirya da hadin guiwar majalisar sarkin Musulmi da sauran kungiyoyin addinin musulunci a Sakkwato.Makalar dai na daga cikin jerin shiraruwan makon Danfodiyo da kungiyar hadin guiwa da majalissar mai alfar sarkin musulmi suka shirya ya kuma gudana a makarantar hardar al’kur’ani da sauran ilmukka ta sarkin musulmi macci dake nan Sokoto, makalar da shugaban tsangayar nazarin addinin musulunci da sauran lamurra na jami’ar Usmanu Danfodiyo dake nan Sokoto ya jagoranci zamanTunda farko da yake magantawa shugaban kungiyar dalibai musulmi na kasa ya bayyana cewa Da’awah hanya ce ta isar da sakon Allah da annabin sa ga al’ummar duniya.A cewar sa domin samun nasarar isar da sakon Allah, ya kyautu mutun ya kasance mai natsuwa, ilimi na abinda zai isar dama na mu’amala da wadanda zai isarwa da sakon.A cewar Amir din kungiyar, mayakan jihadi na daular Usmaniya sun gudanar da Da’awah ta amfani da ilimi, inda ya bayyana cewa Shehu Danfodiyo wanda ya samu ilimi sosai a bangaren shari’a, zamantakewa, addini, ya wallafa daruruwan littafai kan ilimi, al’ada, yayin dan dan uwan sa he Sheikh Abdullahi Bin Fodiyo ya wallafa sama da littafe 10 kan littafin Allah, da ilimin Tajweed, hadisi, Fiqhu, baya ga wadanda dansa Muhammadu Bello ya wallafa na tarihi, ilimin addinin musulunci da da dai sauran su.Shi ma da yake magantawa a wajen taron Farfesa S. O. Rabi'u na sashen nazarin shari’a dake jami'ar Usmanu Danfodiyo dake nan Sokoto ya gabatar da makala mai taken gudunmawar Shehu Usmanu wajen jaddada addinin musulunci a sasssa da dama na kasar nan. Shugaban kwamitin shirya taron Sadaukin Sakkwato, ya bayyana cewa an shirya taron ne da gayyato mahalarta zaron daga sassan kasar nan da wajen ta dan tunatar da juna akan ayukkan su Shehu Usmanu da maitaimakan shi, an kuma gabatar da Daura, kacici- kacici, kasidu da wa'azukkan dare tun farkon makon da ya kare.
ZAHARADDEEN ABUBAKARGWANDU

ALLAH ya kawo muna kashen ta,addanci a najeriya ameen!!!