;
Sama da mutane 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a Jigawa

Sama da mutane 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a Jigawa

Sama da mutane 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a Jigawa yayin da ruwa ke ci gaba da mamaye al’umma a sassan jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawal Shiisu, ya tabbatar da hakan ga manaima Labarai

A cewarsa, mutuwar ta faru ne sakamakon nutsewa, da kwale-kwale, da rushewar gine-gine.

Ambaliyar ruwa na ci gaba da yin barna a jihar Jigawa yayin da al'ummomi da filayen noma suka nutse a yankuna da dama na jihar.

Ambaliyar ta kuma yi illa ga ababen more rayuwa a jihar, yayin da wasu tituna suka katse sakamakon zaizayar kasa, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin neman wasu hanyoyin da za su bi.

Wannan halin da ake ciki yanzu ya sa ɗaruruwan mazauna wurin suka rasa matsugunansu, inda da yawa ke samun mafaka na wucin gadi a gine-ginen jama'a.