;
Shekaru 10 da kirkiro aikin sabuwar sakatariyar Kebbi; Har yanzu aikin cikin halin ni’yasu.

Shekaru 10 da kirkiro aikin sabuwar sakatariyar Kebbi; Har yanzu aikin cikin halin ni’yasu.

Daga Aminu Alhussaini Amanawa a Kebbi

 

Nakan kashe kusan dukkanin albashi na wajen tafiya aiki, da samarwa kaina muhalli, da abinci, saboda nisan wajen da nake aiki.

Kaga ina karkashin ministry of budget tana nan cikin birnin Kebbi, amma department dina na Bagudu tafiyar kilomita 160 zuwa 200, wanda ba zai yu inje aiki kullun in dawo ba, abinda yasa albashin da nake karba baya isa ta dawainiyar tafiya kawai, da abinci da wurin zama doli sai na dan hada da dan buge-buge, saboda ba accomodation kuma maganar gaskiya indaiaccomodation ne ko permernent secretary basu da accomodation indai a Kebbi ne, balle sauran kananan ma'aikata.

                       Sabuwar sakatariya

Usman Muhammad Anache daya daga cikin ma'aikatan gwamnatin Kebbi ke nuna damuwarsa kan yanda warwatsewar ma'aikatu dama sassa ke lakume albashin kananan alhaki wajen kokarin sauke nauyin su na aiki.

Maganar gaskiya rarrabuwar minsitry daban a cikin Birnin Kebbi ya shafi yanda muke gudanar da ayukkan mu a matsayin mu na ma'aikata, musamman bata lokaci wajen aiwatar da ayukkan gwamnati dama tafiyar dasu.

Misali Sakatariyar Gwadan Gwaji tana dauke da ministry of Agric, amma Karda da Cascom da suke under ministry din suna Kalgo, kaga ko aiki ake son yi tsakanin Kwamishina na Agric da GM na KARDA, ko KASCOM, kaga abin zai dau lokaci ko ance wannan zaiyi signing dan tsakanin nan Gwadan Gwaji Sakatariya zuwa KARDA yafi kilomita 10 saboda sai ma ka fita cikin kwaryar birnin Kebbi.

Gama wani misali ministry for basic education itama tana nan a Gwadan Gwaji amma SUBEB tana can hanyar barikin soji kaga nisan yakai kilomita 6.

Itama Environment tana Bulasa kuma nisan zai kai 5 kilomita, amma forestry tana nan kusan government House.

Kaga koda gwamnati xatace samar da motoci dan wannan sufurin anan Kebbi bazai yu ba, saboda duka ministry da hukumomi warwatse suke cikin birnin Kebbi.

Kaga idan kace ka dauki ma'aikatan Karda ka kaisu Kalgo, ka zaga yo, ka Dauko ma'aikatan Kuda, zuwa Emir Usman Haruna road, kazo tudun wada da sauran su kaga ba zai yu ba.

Itama ministry of justice tana nan kusan government House.

Itama Health ministry din tana Gwadan Gwaji amma wasu department dintah nan nan Emir Haruna kusa ga CBN.

Haka education na Gwadan Gwaji amma secondary school managament board na wannan hanyar ta Emir Haruna road kusa ga gidan Sule ba Saura.

Su kuma Higher education, work duka suna Halliru Abdu road inji shi.

                Alon shiga tsohuwar sakatariya

A Shekarar 2012 tsohuwar gwamnatin gwamnan wannan lokacin Alhaji Saidu Usman Nasamu Dakin Gari ta bada kwangilar samar da sakatariyar kan kudi naira biliya 3.8.

Aikin dai a lokacin ya kunshi samar da ginin ofisoshi da zai iya daukar dawainiyar kusan dukkanin ma’aikatun jihar, da ofishin shugaban ma’aikata na jiha, dana sakataren gwamnati baya ga masallatai, wurin cin abinci da dai sauran su.

Yunkurin samar da sakatariyar dai ya biyo ne bayan rarrabuwar ma’aikatu daban-daban dake cikin kwaryar birnin na Kebbi baya ga wadanda ke akwai a Gwadan Gwaje.

Sai dai yayin da aikin yakai kashi 50 na matakin kammaluwa gwamnatin a watan Nuwamban 2014 ta sake sabunta kwangilar aikin zuwa naira biliyan 7 da doriya, aikin da ya cigaba da tafiyar hawainiyar har zuwa lokacin da gwamnan jihar mai ci yanzu Abubakar Atiku Bagudu ya sake sabunta aikin kwangilar a karo na biyu.

Masallacin Da ake Ginawa Dake Cikin Sakatariyar

Wannan ko ya biyo bayan bukatar sake duba aikin kwangilar da kamfanin dake aikin na RockWell Development Nig LTD. (Kamfanin ‘yan china) lamarin da yasa gwamnatin jihar watsi da wannan bukatar.

Kabawa sun nuna damuwa

A shekarar 2019 dinbin masu kishin jihar Kebbin ne suka rika fitowa a kafafen sada zumunta na zamani, inda suke nuna damuwa kan watsi da aikin na gina sakatariyar.

Yayin da wasu ke dasa ayar tambayar kan cewa, ko me yasa gwamnatin data fito da aikin kasa kammala shi? suna masu cewar bai kyautu ba ace gwamnati ta fito da aikin da bata iya kammalawa.

Bagudu Ya Fitar da Kudi Domin Kammala Aikin

Sai dai a shekarar 2020 gwamnatin jihar mai ci yanzu karkashin jagorancin Abubakar Atiku Bagudu, ta amince da fitar da naira miliyan N949,198,886.26, domin bawa kamfanin Rock Well Development Nig LTD ya samu damar kammala aikin ginin sabuwar sakatariyar Gwadangaji dake Birnin Kebbi.

A wani bayani da mai Magana da yawun gwamnan Abubakar Mu’azu Dakingari ya fitar, ya Ambato kwamishinan ayukkan Alhaji Abubakar Chika Ladan na cewa fitar da kudin ya biyo ne bayan cimma matsaya da gwamnatin tayi da acewar kwamishinan aikin idan an kammala shi zai tallafa matuka wajen gudanar da ayukka a Kebbi.

‘Yan Jiha Na Nuna Damuwa

Shehu Isa S/Kudu wani mai fafutikan cigaban jihar Kebbi ne, ya bayyana rashin jin dadinsa kan watsi da aikin, duk kuwa da cewa an warewa aikin makuddan kudade domin kammala sa.

Dangwagwarmaya Shehu S/Kudu

“Yakamata ace gwamnatin Kebbi ta cire duk wani abu, tazo ta kammala aikin nan, sa’ilin da saura ke cigaba da kasancewa a hannun rabbu ka wada ta mu, ka duba gwamna Atiku Bagudu ya amince da fitar da sama da Nairamiliyan 900 domin kammala aikin, amma ka duba har yanzu aikin shiru kakeji tamkar an shuka dusa”

“Maganar gaskiya kudaden nan da aka fitar sun isa ace an kammala wannan aikin dama dangoginsa, sai dai a maimakon haka gwamnati ta cigaba da bayar da sababbin kwangiloli a zaman majalissar zartaswa”

Shehu S/Kudu hakama yayi zargin cewa, wannan abun damuwa ne, kuma abin Allah waddai cewar sa.

Ko Me Yakawo Tsaiko Ga Kammala Aikin?

A zantawa ta musamman da nayi da kwamishinan ayukka na jihar Kebbi Alhaji Abubakar Ladan kwamishinan ya zargi kamfanin dake aikin da kawo tsaiko ga kammaluwar sa, kasantuwar kamfanin ya kasa komawa bakin aikin duk kuwa da makuddan kudaden da aka ware masa.

“Kamar yanda ka sani wannan aikin gwamnati mai ci yanzu ta gajesa ne ga tsohuwar gwamnati data bada kwangilar yinsa tun a shekarar 2012 kan tsabar kudi Naira biliyan 3 da doriya, wanda daga bisani ta sake sabun kwangilar aikin zuwa naira biliyan 7.7 wato kusan dai kaso 100 na adadin farko da aka somo kwangilar”.

Sai dai bayan shigowar gwamnatin mu, mai girma gwamna ya cigaba da aikin sabunta kwangilar da sama da Naira miliyan N900 da manufar kammala aikin, sai dai yan watanni da cimma matsaya da kamfanin kamfanin ya kasa dawowa domin cigaba da aikin, bayan bukatar sake sabunta kwangilar a karo na biyo abinda gwamnatin mu taki, saboda mun lura cewa kudin da aka samarwa kamfanin sun isa kammala aikin, kwatankwacin kudin da aka samar domin gina assibitoci, makarantu da dai sauran su.

Alhaji Abubakar Ladan

“Saboda haka muna shawartar kamfanin da yazo domin cigaba da aikin, abinda yaki kuma muna kan wannan matsalar”.

Dan haka idan kamfanin ya kasa komawa domin cigaba da aikin, zamu duba daftarin da tanadin dokoki domin muga me doka tace idan bukatar soke kwangilar ce mafita zamuyi, ko samar da kamfanin da zai iya kammala aikin.

“Aikin ba karami bane, yana da matukar muhimmaci, kaga ko nan ma’aikatar ayukka muhallin mu makarantar sakandiri ce baya, da muka mayar a Jega domin mayar da wannan wajen muhallin mu, amma insha Allah zamu kammala aikin kafin karshen wa’adin mulkin gwamna Bagudu.

Me kamfanin Rock Well ke cewa?

Duk kokarin da nayi na jin tabakin kamfanin yaci tura, sai dai a wata zantawa da Kakakin kamfanin dake Kebbi Muhammad Shehu Nasir ta wayar tarho, kakakin ya sheda man cewa lallae kamfanin ya tattara nasa da nasa ya bar jihar, kasantuwar gwamnatin jihar ta kasa sake sabunta kwangilar kamar yanda suka nema a karo na biyu saboda hauhawar farashin kaya.