;
SHUGABA BUHARI: KADA KU BADA KO SISI GA MASU SHIGO DA KAYAN ABINCI DA TAKI KASAR NAN

SHUGABA BUHARI: KADA KU BADA KO SISI GA MASU SHIGO DA KAYAN ABINCI DA TAKI KASAR NAN

By SulfidoneA dai dai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke tafiyar da Shirin Inganta Tattalin Arzikin da tsara muradun da ake bukatar Cimma da shirin Samar da Abinci ta kasa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bada izini wa Babban Bankin kasa CBN da "Kada ta bada ko sisin kobo " cikin ajiyar da kasar ke dashi don shigo da kayan abinci da takin Zamani. A yayin taron Majalisar Samar da abinci ta kasa daya gudanar a fadar Gwamnati dake Abuja, Shugaban kasa Buhari ya kara jaddada Umarni daya fadi ga Babban Bankin kasa tun a farkon fari, yace ya mika wa Bankin a Rubuce cewa "Kada su bada kudi don Shigo da abinci kasar."Shugaban kasa yace, Ya karfafa bukatar kara bunkasa abinci da ake Noma a gida, " Daga kamfanoni Uku kadai da muka zo muka samu suna aiki a kasar, Yanzu munada Kamfanonin Sarrafa Takin Zamani 33 dake aiki. Bazamu biya ko sisin kobo ba ga Asusun mu na ketare don shigo da takin Zamani a kasar. Zamu karfafa Kamfanonin mu na cikin gida."Bugu da kari, Shugaba Buhari ya kuma bada Umarnin ga masu samar da Sinadaran Sarrafa takin zamani dasu ke samar wa kai tsaye ga Gwamnatocin Jihohi saboda kauce wa 'Yan kasuwa masu harkan dake kawo koma baya ga kokarin Nasarar Samar da Takin ga Manoma a farashi mai sauki.Shugaban kasa ya Shawarci 'yan kasuwa masu zaman kansu dasu kauce wa shigo da kayan Abinci don samun daman Dogaro ga Babban Banki gurin Samun Chanjin kudi, yace "Kuyi amfani da kudin ku gurin gogayya da Manoma", a Maimakon amfani da Asusun kasa na ketare don Shigo da kayan Abinci dazai kawo Nakasu ga kokarin Manoman mu." Muna da Matasa masu Jini a jika da dama dake da aniyar yin aiki wanda kuma hanyar Noma shine kawai Madogara. Akwai aiki dake gaban mu sosai na ganin mun tallafawa Manoman mu," Inji Shugaba Buhari.Taron wanda Shugaban kasa ya jagoranta da halartan Sauran Muhimman Membobin Majalisa, anyi Bayani kan yadda Matsalar Abinci ke yaduwa a kasa.Musamman, Mahalarta taron sun hada da Mataimakin Shugaban Majalisar kuma Gwamnan Jihar kebbi Atiku Bagudu, Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban kasa Prof. Ibrahim Gambari, da Wakilcin Gwamnoni dai daya daga Shiyar Siyasa Shidda dake kasar nan, Jigawa, Plateau, Taraba, Ebonyi, Lagos, dakuma jihar Kebbi, Sun Samu Halartan taron.Ministan Kudi da tsara kasafin kasa, Dr Zainab Ahmed, ta zayyano Matakai da Gwamnati ke gabatarwa don Dakile yawan Koma baya da ake samu sakamakon Annobar Cutar Korona ga Shirin Cigaban Tattalin Arzikin Kasa (NESP).Sauran abubuwa data gabatar, Ministan ta tsakura cewa Gwamnati zata samar da Sabbin filayen Noma dayakai Kidada Dubu Ashiri 20,000, zuwa Dubu Dari 100,000 a kowace Jiha da Mara baya wa Samar da Guraren fara Sarrafa amfanin Gona wanda haka zai Samar da Miliyoyin guraben aiyuka kai tsaye.Ta kuma Lissafo Samar da aiki na kai tsaye har guda Dubu dari bakwai da Saba'in da hudu 774,000 Alal akallah matasa Dubu Daya 1,000 a kowace karamar Hukuma, da Gina Rukunin Gidaje Dubu Dari Uku 300,000 a ko wace Shekara don samar da guraben aiki ta hanyar Kamfanonin Gine gine, dama kuma hada Mutane Miliyan Ashirin da biyar 25,000000 da wutan Lantarki da kuma Sabon Shirin nan na Samar da Lantarki ta Hasken Rana ga gidaje, Solar Home System (SHS) da aka tsara zai kai lantarki ga Gidaje Miliyan biyar 5,000000.Dakta Ahmed ta kumayi Jawabi akan Hadakan kasuwanci da Bankin Duniya don Samar da kudaden gudanar da kasuwanci ga Jihohi don kara inganta Aiyukan kiwon lafiya.Tace, Don Saukaka wahalan karancin walwalan kudi a hanun Mutane, Gwamnati zatazo da wasu tsare tsare Samun bashi mai saukin ga Masu aikin Kani kanci, Tailoli, Kananan masu Sana'a, Kananan 'yan kasuwa da sauran masu Sana'oin da bai kai ya kawo ba.Ministan ta kuma kara da cewa, Gwamnatin Tarayya zata kuma samar da Tallafi ga Kanana da Matsakaitan 'yan kasuwa don taimaka musu gurin Cigaba da rike ma'aikatan su da habbaka abubuwa da suke Sarrafawa.Dakta Zainab Ahmed, tayi bayani filla filla cewa sakamakon Amince da ware Naira Tiriliyan 2.3 (N2.3 trillion) don kara kuzarin kasuwanci wanda Shirin Cigaban Tattalin Arzikin Kasa (NESP) ya bada Shawarin ayi, za'a kara fadada matakan da kara samar da Guraben aikin yi a fannin kasuwancin Zamani, da shirin kara Fadada Shirye shiryen samar sa guraben Dogaro (National Social Investment Programmes)ta hanyar kara yawan Masu imfana da Shirye Shiryen kamar masu imfana da Cash transfer, N-Power Volunteers, Market Moni dakuma shirin Trader Moni.A gabatar wa da yayi Ministan Gona, Alhaji Sabo Nanono ya fadawa Majalisar cewa, Ana sa ran Samun karuwan amfanin Gona dukda Ambaliyar ruwa da'aka samu a Arewa da karin samun Ruwan sama da ba safai ba a Kudu.Ya kafa hujja da ba'asin kasuwa da aka gudanar na baya bayan nan, daya nuna an fara samun koma bayan haw hawan farashi kayan Masarufi.A Bangaren sa, Sakataren Gwamnatin Tarayya Mista Boss Mustapha kuma Shugaban Kwamitin Shugaban kasa na yaki da Cutar Korona, Presidential Task Force on COVID-19 ya habarto samun koma baya da Annobar ta kawo akan rayuwar yau da kullum na 'yan Kasa, yayin kuma da Babban kanturola na Hukuma hana fasa kwafri na kasa Comptroller-General of Customs, Col Hameed Ali (Rtd), ya bayyana fatan na ganin an sake bude iyakokin kasar sakamakon Cigaba da aka samu ga kasashe makota akan Jami'an Sintirin iya kokin kasashen na Hadin Gwaiwa, wanda yana daya cikin Manyan Sharadodin Najeriya na sake bude iyakokin kasar.