;
SHUGABA BUHARI YA BUDE AIKIN LAYIN JIRGIN KASA MAI TSAWON KILOMITA 326  DAGA ITAKPE ZUWA AJAOKUTA ZUWA WARRI DON FARA ZIRGA-ZIRGA.

SHUGABA BUHARI YA BUDE AIKIN LAYIN JIRGIN KASA MAI TSAWON KILOMITA 326 DAGA ITAKPE ZUWA AJAOKUTA ZUWA WARRI DON FARA ZIRGA-ZIRGA.

By SulfidoneBayan Shafe sama da Shekaru 30 da watsi dashi, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Talata ya bude aikin layin jirgin kasa mai tsawon kilomita 326 da Gwamnatin sa ta Shimfida tun daga Itakpe zuwa Ajaokuta zuwa Warri, don fara zirga zirgan fasinja da samar da wata hanyan sufurin kayaki, kaddamar wan ya gudana a gurin da cikin 'yan kwana kinnan aka mata lakabi da Goodluck Jonathan Railway, dake Agbor (Owa-Oyibu) jihar Delta.A yayin kaddamar da layin Dogon daya hada Itakpe da Warri ta Na'urar Zamani, Shugaba Buhari ya bada Umarni ga Ma'aikatar Sufuri da suyi Shimfida layukan jiragen kasa a Dukkan Tashoshin Ruwan kasar nan, daga Apapa zuwa Tin Can, dana Warri, Onne, da Tashar ruwan Calabar don kawo cigaba da kara inganta harkokin Sufuri da kara samar da kayakin karfafa Tattalin Arziki.Shugaban kasar ya bayyana cewa Gwamnatin sa, ta fahimci Muhimmancin Samar da Layin jiragen kasa a matsayin wata Muhimmin hanyar Sufuri da kuma kashin bayan taimaka wa Masana'antu da cigaban Tattalin Arziki."A Dalilan haka" Na amince da bada fifiko ga muhimman hanyoyin jiragen kasa ga koyin Sabbi ko sake gyara wasu dake akwai, don cimma nasarar Samar da wadatuwar harkokin Sufurin jirgin kasa don taimakawa harkokin Kasuwanci da Masana'antu na kasa."Gudanar da Gagarumin aikin Layin Dogo, a yau na samu damar Kaddamar da aikin Layin jirgin kasa daga Itakpe daya biyata Gari mai Babban kamfanin Sarrafa Karafa Ajaokuta zuwa Warri, kuma wannan wani Muhimmin hanya ce ga tattalin Arzikin kasa kasan tuwa Cibiyar ce ta Hanyar Jiragen Kasa."Wannan Gwamnati tuni tariga kuma ta amince da hada wannan Layin Dogo ya kara tsawaitashi daga Itakpe zuwa Abuja, Daga nan kuma, zai hada yankin Arewacin kasar da kara hada yankin Kudu da Tashar ruwa ta Warri," cewar Shugaba Buhari.Shugaban kasar ya nuna Gamsuwar sa kan aikin, Wanda zai zamo muhimmin mahada na shiyar Kudu maso Kudu a kasar da Shiyar Arewaci, za'a kammala wannan aiki a lokacin Mulkin Gwamnati mai ci."Zai hada mutane daga bangarori da dama dama fadada harkokin kasuwanci da Masana'an tu, wanda zai kuma kara Inganta rayuwar 'yan kasa," Inji Shugaban.Shugaba Buhari ya tuna da 'yan Najeriya Maza da Mata da suka mika kansu gurin Gina kasa da cigaban ta, inda aka akayi lakabi ga Tashoshi 11 da sunayen wasun su da suk chanchanta, Shugaban ya Jero Sunayen Tashoshin kamar haka: Tashar Itakpe Adamu Attah, Tashar Abubakar Olusola Saraki Ajaokuta, Tashar Augustus Aikhomu Itogbo, Tashar George Innih Agenebode, Tashar Anthony Enahoro Uromi, Tashar Tom Ikimi Ekehen, dakuma Tashar Samuel Ogbemudia Igbanke.Saura sun hada da Tashoshin; Tashar Goodluck Jonathan Agbor, Owa-Oyibu. da Tashar David Ejoor dake Abraka, da Tashar Michael Ibru dake Opara da TasharAlfred Rewane dake Ujevwu, da Layin Jirgin kasa na Michael Akhigbe dake Agbor.Shugaba Buhari ya ja hankalin Dukkan 'yan Najeriya dake a fannin Kasuwancin Sufurin, Musamman a Fannin Sufurin Jiragen Kasa da su cigaba da mara baya wa Gwamnati a kokarinta don cimma wasu aiyukan shimfida layin Jiragen kasa.Ya kuma jero irin goyon baya na Dukkan wadanda suka tabbatar da yin Nasarar wannan abin cigaba, na Samar da babbar tashar Layin Jiragen kasa, bayan Shafe Shekaru sama da 30, lokacin da aikin yasamu nakaso."Ina rokon wadanda ke aiki akan wannan hanya dasu bada hankali gurin kulawa dashi wanda hakan yazamo wajibi domin a jima anacin moriyar sa." A hanu guda kuma, Ina kwadaita wa Dauran Fannoni wadda su zasu fara imfana da wannan aikin hanyar jiragen kasa, cikin su da bangaren Karafa, Masu ruwa da tsaki a Fannin Noma da harkokin Ma'adinai, dama Garuruwa da aikin ya tsara ciki da subada kulawa ga aikin da kara fadada cin gajiyan aikin da za'a samu, Wanda yanzu yazo musu har gida."Wannan aiki zai kara inganta harkokin kasuwanci da samar da gurin safarar karafa." Dukkan wadan nan, Ina fata zai inganta Dama dake akwai na Masana'antu dama kara Habbaka samar da aikin yi," cewar Shugaba Buhari.Shugaba Buhari yace, Hasashe yayi nuni da cewa fara gudanar da aiki Layin dogo na Jirgin kasa daga Itakpe zuwa Ajaokuta zuwa Warri kusan Mutane Miliyan guda zasuyi sufuri a hanyar cikin kowace Shekara, da sufurin kayaki kimanin Ton Miliyan 3.5 cikin kowace Shekara, wanda ya kunshi Sufuri a kan hanyar dama koma bayan sa.Ina Taya Ministan Sufuri Hon. Rotimi Chibuike Amaechi Murna, da tawagar sa, kan samun Nasarar kammala wannan aiki, Shugaban kasa ya yabawa wa Garuruwa da aikin ya biya ta ciki kan Nuna Hakuri yayin aiwatar da wannan aikin bayan shafe shekaru sama da 30 ana Dako don kagin wannnan aiki a zahiri.Shugaban ya kuma, yabawa Garuruwa da aiki ya biya ta ciki kan hadin kai yayin kammala wannan aiki na Gwamnatin Tarayya.Ya bada tabbaci wa 'yan Najeriya, cewa Wannnan Gwamnati zataci gaba cikin Dan kudade da take samu ta cikin ka'ida tab hada cibiyan Masana'antu da Kasuwanni don karfafa kasuwanci, da samar da arziki da guraben aiki.Cikin Jawabin sa, Gwamnan Jihar Delta Dr Ifeanyi Okowa, ya jinjina wa Rashin nuna banbanci a fannin tafiyar da mulki na Shugaba Buhari, yace " abin alfahari da farin ciki ganin an kammala wannan aikin shimfida layin Jirgin kasa a lokacin Mulkin mu.""Al'umman jihar Delta suna cikin farin cikin wannnan rana," yace, ya kara da cewa kasar Ika tana murna da sanya Sunan Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a layi da Tashar Jirgin kasa na Garin Agbor.Gwamna Okowa ya bukaci 'yan kasuwa masu zaman kansu dasuyi imfani da wannan dama mai cike da tarihi ta hanyar kafa masana'ntu dazai Samar da Guraben aikin yi, don dakile matasa dake shiga Mumunar aika aika."Ya zamo wajibi ga Gwamnatin Tarayya ta nemi hadin kan jihohi gurin Samar da tsaro don tsare layin dogo na jiragen kasa.Cikin Jawabinsa, Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki, ya taya Shugaban kasa Murna sakamakon kammala wannan aiki, yace wannan abin yabawa ne musamman kwanaki kadan ya rage kasar tayi bukin cika shekaru Sittin da samun 'yanci, Shugaban kasa yayi nasarar Samar da Muhimman manyan Aiyukan gina kasa, " Gare mu a jihar Edo muna cikin Murna mara misaltuwa kancewa munada aiyuka da aka kammala su, kana kuma zamuci gaba dayin aiki kafada da kafada dakai don imfana da wannan aiyuka, inji Gwamnan.Gwamnan jihar Edo ya bukaci Ministan Sufuri da ya isar da aikin layin jirgin kasa zuwa cibiyar kasuwanci na Birnin Benin don saukaka sufurin kayaki zuwa yankin Arewacin kasar.Cikin Jawaban sa, Minista Amaechi, yace aikin Gwamnnatin Najeriya ce ta samar da kudaden gudanar dashi, ya kara da cewa kaso 8 cikin 10 na Tashoshin jiragen na a yankin Arzikin mai na yankin kudu maso kudu a yankin Niger-Delta na kasar."Babu wani bashi da muka ciwo don gudanar da wannan aiki, An samar da kudaden ne daga kasafin kudi da aka tanada kuma na samu amincewar Shugaban kasa kan na sake duba aikin kima na kammala shi cikin lokaci kankani, cewar Ministan.Bisa ga Ministan Sufuri, wannan aikin anfarashi tun zamanin Mulkin Soji a shekarar Alif dubu daya da Dari tara da Tamanin da Bakwai 1987. to amma" tuntuni akayi watsi da aikin da lalatar dashi sosai," kafin da yanzu Gwamnatin Buhari ta waiwayeshi.Femi Adesina:
traulge

A simple sensorymotor neuron circuit is shown in Fig. https://oscialipop.com - viagra and cialis online Buy Now Tab Isotretinoin Order Plavix From Canada Bfaalk <a href=https://oscialipop.com>Cialis</a> Cephalexin Dosing In Dogs https://oscialipop.com - viagra cialis online Hrmkpj