;
SHUGABA BUHARI YA JINJINAWA JANARAL GOWON

SHUGABA BUHARI YA JINJINAWA JANARAL GOWON

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Bayyana Tsohon Shugaban Kasa na Mulkin Soji Jenaral Yakubu Gowon a Matsayin " Jarumi Dan kishin kasa wanda ya mika wuya gurin hadin Kai, mara misaltuwa cikin bangarori Maban-banta a tarihi."Cikin wata Sanarwa da aka fitar a Abuja, ranar lahadi don bikin Zagowar Ranar Haihuwan sa Shekaru Tamanin Da Shida 86, Shugaba Buhari yayi Jawabin cewa " Rawar da Janaral Gowon ya taka cikin tarihin Siyasa da aiyukan cigaba kamar Zanen Dutse ne da bazai goge ba."Shugaba Buhari yace "A Matsayin Matasan Babban Jami'in Soji, da yawan mu Muna Daukan Gowon a matsayin abin koyi saboda kishin kasan sa, Jajircewa gurin Hadin kai da Kan kan da kai." Bisa ga Shugaban kasa, "Yakin Basasan kasar ya fito fili da irin basira dake tattare da Janeral Gowon a Matsayin Shugaba mai hangen Nesa wanda ya sanya kishin kasa Najeriya sama da Bukatun kan sa."Ya nunar da cewa "Tsohon Shugaban Gwamnatin Soji ya Jagoranci Kokarin tattaunawar Sulhu ga kasa abin birgewa a karshen yakin Basasa don saukaka fushi da samun saukin raunin zuci sakamakon rikicin dayayi Sanadiyar Mutuwar 'yan uwa."Shugaba Buhari ya kara da cewa "Jenaral Gowon Dayane cikin Shugaban ni masu kyan gani dana bata sani wanda ya birge dayawan Shgaban ni masu tasowa."Ya kara da cewa "Har ma ga abinda yashafi Afirka, dayawan Shugabanni a Nahiyar ya birgesu kan yadda ya tafiyar da al'amura bayan yakin Basasan a tafarkin tsare tsaren mai taken 'Ba wanda yayi Nasara, Ba wanda yayi Rinjaye." Shugaban kasa yayi Addu'a "Dai dai wannan Lokaci da yake cika Shekaru 86, 'yan Najeriya bazasu taba Mancewa da Gudumawa Mara Misaltuwa da Jenaral Gowon ya bada gurin Hadin Kai da Cigaban Najeriya. Allah yaci gaba da masa Albarka da bashi koshin Lafiya da dukkan karfin Jiki da ake bukata don kara fahimtar Bauta da Dawainiya ga Al'umma,"