;
SHUGABA BUHARI YAYI ALWASHIN CEWA, HARI KAN MAKARANTAR HORON SOJI  TA NDA

SHUGABA BUHARI YAYI ALWASHIN CEWA, HARI KAN MAKARANTAR HORON SOJI TA NDA

Harin da aka kaddamar akan ginin Makarantar Horon Soji ta NDA a ranar Talata, a maimakon ya sanyaya gwiwa kan irin hazakan Jami'an Sojin mu kamar yadda maharan suka so, zai kara azamar ga aniyar dake nan don kawo karshen aiyukan Ash-sha a Ƙasar, Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka. Ya nunar da cewa Harin, wanda yayi sanadin rashin rayuka, yazo a daidai lokacin da Sojoji suka sanya Masu tada kayan baya, Ɓarayin daji, Masu garkuwa da Mutane da Sauran nau'in masu aika-aika ja da baya, Shugaban kasa ya ce, Mumunar matakin da suka dauka zai kara hanzarta sake tsuguni wa Munafukai a harkan Shugabanci.Wanda membobin tsaro sunyi na'am don ganin an kammala dasu cikin kankanin lokacin daya dace. Ya jajanta wa Iyalai da suka rasu Ƴan-uwan su, yayi addu'a Allah yaji kan su, Shugaba Buhari yasha Alwashin cewa, Mamatan baza su tafi haka kawai ba, akwai Sakayya na wannan Mumunar aikin su, wanda daga bisani zai tsaf tace halin damuwa a kasar, da Ƴantar da harkan Shugabanci daga masu aikin gangan, da nufin aikata mugunyar aiki. Shugaban Ƙasa ya godewa duk Ƴan-Nijeriya wanda suka Daraja da yin farin cikin irin kokarin sojojin mu, da jan hankalin masu Mumunar Siyasar tsana da tsoro kan su guji wannan aikin, ya nuna cewa, in banda masu iza wutar al'amarin, wannan lokaci ne da duk masu ƙishin ƙasa, da mutane masu fatan Alkhairi, zasu goyi baya da karfafa gwiwa ga wadan-da ke sahun gaba, don yaki da Mugunyar aiki a doron kasa.Femi Adesina:Mashawar ci Na Musamman ga Shugaban Kasa a Fannin Yada Labaru da Wayar da kan Jama'a.25th ga watan Ogusta, 2021