;
Breaking
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Dauki Makati Akan Matsalar Karancin Abinci

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Dauki Makati Akan Matsalar Karancin Abinci

By SulfidoneShugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Alhamis a Abuja yace, Annobar Cutar Korona ya bayyana irin Mataki na shiri da kasar tayi kan Karancin abinci, wanda ya nuna irin hikima dake tattare da Shirin Gwamnatin Tarayya na Dabbaka Dogaro da kai, kan samar da Abinci don kauce wa Matsalar Karancin abinci.A lokacin dayake Magana gurin Taron Majalisar kasa kan Kayan Masarufi, taron data gudana a fadar Gwamnati, Shugaban kasa Buhari ya nunar da cewa, Akwai Bukatar akara kokari sosai don kara samar da kayan abinci da Dogaro da kai, da bada tabbacin Gwamnatin Tarayya na cigaba da dabbaka Shirye Shirye dazai bada fifiko kan zuba jari a harkan Noma."Annobar Cutar Korona ya kara wayar wa Duniya kai fiye da koma a tarihi kan yadda yazamo dole kasashe su farka don bada kulawa ga tsarin samar da Abinci. Yakuma fayyace yadda yakamata kasashe su rage Dogara da juna." Cikin Shekaru biyar na baya baya da suka Shude mun cimma Gagarumin Nasarori. Duk da rugujewar tattalin Arziki da kaso 6.1 cikin Dari a zangon farko na Shekarar 2020 sakamakon Cutar Korona. Bangaren Noma yasamu cigaba da habaka saboda Shirye Shirye da Manufofin Gwamnati."Shugaba Buhari, Wanda ya jinjina wa Manoma kan Gudumowa da suka bada gurin dai-daituwar Kayan abinci, Shugaban yace Kyan Damina da ake samu yakamata ya zamo wani dama dazai kara karfin gwaiwa ga Manoma don rungumar Noma a matsayin abin yi."Ina farin ciki kasan cewa da yawan 'yan Najeriya suna imfani da damar dake akwai a harkan Noma da kasuwancin sashen Noma. Ina son na baku tabbacin cewa wannan Gwamnati zataci gaba da Mara baya ma wadan nan Shirye Shirye da saura da dama dazasu zo nan gaba."Shugaban kasar yakuma ce za'a kara kokari ta hanyar sabbin Dabarun Noma dazai kara wadatuwar abinda ake samu."Don bada kariya wa zuba jari a bangaren Noma da kara inganta kwarin gwaiwar Manoma mun Dauki Dubbannin Masukula da sashen Noma da Miniyan tar da karkara ta yadda zasu zamo masu samar da Arziki ta hanyar basu daman samun bashi da kayakin Noma ga Manoman Karkara dama gina hanyoyi da zai saukaka musu gudanar da aiki." Cikin 'yan Shekarun nan Mun aiwatar da aiyuka ciki harda gina tsarin Runbun aje Kayan masarufi wanda kwanan nan muka bada wani kaso mai tsoka don Dakile Illar Annobar Cutar Korona ga Talakawa magidanta dama Kamfanoni," Inji Shugaba Buhari.Shugaba Buhari ya jajanta wa Manoma da Iyalai da suka rasa 'Yan uwa a ambaliyar Ruwa daya auku kwanan nan a kasar, Da bada tabbacin Gwamnati data taimaka wa wa'inda lamarin ya shafa.