;
Shugaban Kasar Sri Lanka Ya Yi Murabus

Shugaban Kasar Sri Lanka Ya Yi Murabus

Bayan kai ruwa rana tsakanin Al’umma da wani bangare na Mahukunta a Sri Lanka, yanzu haka dai Shugaban Kasar Gotabaya Rajapaska ya sauka daga mulki a hukumance.

Dandazon al’ummar kasar sun afka Zanga-zangar neman sauyin shugabanni a kasar sakamakon matsin tattalin arziki da ya haifar da hauhawar farashi da cin hanci tsakanin masu rike da madafun iko a Sri Lanka.

Mr Rajapaska ya sanarda murabus dinsa a rubuce daga kasar Singapore cikin sakon Email da ya aike wa Kakakin Majalisar Dokokin Kasar.

Rahotanni sun tabbatar da cewar wannan shi ne karo na farko da shugaba ya yi murabus a tarihin kasar tun lokacin da kasar ta karbi tsarin mulki na shugaba mai cikakken iko a shekara 1978.