;
Shugaban Nijeriya  Muhammadu Buhari, ya bai wa wasu yan kasashen waje 286 takardar shaidar zama yan Nijeriya.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bai wa wasu yan kasashen waje 286 takardar shaidar zama yan Nijeriya.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bai wa wasu yan kasashen waje 286 takardar shaidar zama yan Nijeriya, inda ya bukace su da su kasance yan na gari domin cin gajiyar duk wani hakki da alfarmar da aka ba su.

Shugaba Buhari, ya bayyana cewa daga cikin ‘yan kasashen waje 286 da aka bai wa takardar shaidar zama ‘yan Nijeriya, 208 sun karbi takardar shaidar zama ‘yan kasa, yayin da 78 suka samu takardar shaidar rajista.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, Buhari ya bukace su da su bayar da gudumawa mai kyau kuma mai amfani ga ci gaba da jin dadin al’ummomin da suke zaune a kasar nan, inda ya kara da cewa a matsayinsu na ‘yan kasa dole ne su kasance masu bin ka’idojin kasa da kasa da ka’idar aiki.