;
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana farin ciki kan nasarorin da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar ke samu wajan yaki da fataucin miyagun kwayoyi.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana farin ciki kan nasarorin da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar ke samu wajan yaki da fataucin miyagun kwayoyi.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana farin ciki kan nasarorin da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar ke samu karkashin jagorancin Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya.

Ya kuma yaba wa Buba Marwa musamman a kan wani samamen baya-bayan nan da jami'an hukumarsa suka yi inda suka kwato kusan kilogram 2,000 na hodar iblis.

A ranar Litinin ne hukumar NDLEA ta ba da sanarwa kan abin da ta kira kame mafi girma na hodar iblis a lokaci daya a tarihin yaki da miyagun kwayoyin kasar, inda jami'anta suka kai samame wani gidan ajiyar kaya da ke Ikorodu a Lagos tare da kama kilogram 1,855 na haramtacciyar kwayar da ta kai kimar naira biliyan 190.

Wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun Buhari ya fitar ta ambato shugaban na Najeriya daga birnin New York inda yake halartar taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya lokacin zantawa ta wayar tarho da shugaban hukumar hana ta'ammali da kwaya yana cewa labarin wawan kamun da NDLEA ta yi ya faranta masa rai.

Buhari ya kuma yaba wa kwazon Janar Buba Marwa wajen kakkabe annobar sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya