;
Zaa Sake Nemo Rancen sama da Naira Tiriliyan Hudu A Nigeria

Zaa Sake Nemo Rancen sama da Naira Tiriliyan Hudu A Nigeria

Ministar kudi a Nigeria Hajiya Zainab Ahmad ta bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta nemi majalisu dasu amince mata ta kara nemo bashin sama da Naira Tiriliyan hudu domin gudanar da manyan ayyukan dake cikin kasafin kudin wannan shekarar. Bashin da idan an karba zai kara yawan basukan da Gwamnatin tarayya ta karbo zuwa sama da Naira Tiriliyan Talatin da biyu, zai kuma kara sarkake kasar a bangaren gudanar da rayuwa cikin yanci. Sai dai Gwamnatin ta bayyana cewa nemo bashin yq zama dole sakamakon manya manyan ayyukan da take son cigaba da gudanarwa wadanda ta tsara zatayi a kasafin kudin wannan shekarar 2020.