Kotu ta Dakatar da Daukar Sabbin Jami’an ‘Yan sandan Najeriya.


Kotu ta Dakatar da Daukar Sabbin Jami’an ‘Yan sandan Najeriya.

Wata kotu dake birnin tarayya Abuja ta umarci Supeta Janar na ‘yan sanda Mohammed Adamu, da hukumar dake kula da lamuran ‘yan sanda PSC, su dakatar da daukar sabbin jami’an hukumar dubu goma dake gudana a halin yanzu.

Tun da farko dai hukumar PSC ce ta shigar da karar a kotu, inda take bukatar a dakatar da IG Adamu akan kokarin da yake na daukar ma’aikatan, saboda a cewar ta hakan kamar karbe ikon hukumar ne.Comments


Post Your CommentLocal News

Foreign News


© 2020 Copyright: visionfm.ng