Kamfanin ZTE Ya Hada Kai Da Kamfanin MTN Wajen yin Gwajin fasahar 5G


Kamfanin ZTE ya hada kai da kamfanin MTN wajen yin gwajin fasahar 5G a Uganda

Kamfanin sadarwa na ZTE na kasar Sin da takwaransa na kasar Uganda MTN sun shirya bikin kaddamar da gwajin fasahar 5G a birnin Kampala, hedkwatar kasar a kwanan baya, inda firaministan kasar Ruhakana Rugunda, da darektan zartaswa na kwamitin aikin sadarwa na Uganda Godfrey Mutabazi, da babban mai jagorar kamfanin MTN Wim Vanhelleputte gami da Yi Yahua, mataimakin shugaban kamfanin ZTE mai kula da harkokin kudancin Afirka suka halarta.

A yayin bikin, Ruhakana Rugunda ya yi jawabi inda ya bayyana cewa, gwamnatin Uganda tana goyon bayan bunkasa sabuwar fasaha, a kokarin warware matsalolin da ake fuskantar a zaman rayuwa. Yana sa ran ganin fasahar ta 5G za ta kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta Uganda.

Godfrey Mutabazi ya nuna cewa, masu sa ido kan aikin sadarwa na Uganda suna kokarin kafa manyan tsare-tsare don goyon bayan ci gaban fasahar 5G a kasar. Hakan zai taimakawa Uganda ta zama ta farko a gabashin Afirka wajen yin amfani da fasahar 5G, kana ta zama ta uku a Afirka baki daya, baya ga kasashen Afirka ta Kudu da Nijeriya.Comments

01-07-20, 7:18 pm

Shamsu

Yayidaidai

Reply Like

07-05-20, 10:20 am

Murtala musa

Is alright may God help us for our daily need

Reply Like


Post Your CommentLocal News

Foreign News


© 2020 Copyright: visionfm.ng