Governor Aminu Waziri Tambuwal ya bayarda umurnin rufe daukacin Makarantun dake jihar nan na tsawon kwanakki 30.


Governor Aminu Waziri Tambuwal ya bayarda umurnin rufe daukacin Makarantun dake jihar nan na tsawon kwanakki 30.

Rufe Makarantun dai zai soma ne tun daga ranar litinin ta makon gobe.

Matakin rufe Makarantun ya biyo bayan wani taro da gwamnonin arewa suka gudanar jiya a kaduna
inda aka amince a rufe Makarantu a jihohi tara na arewa da suka hada da sokoto, da Kebbi da Zamfara da kano da katsina da kaduna da jigawa da kwara da Kuma kogi.

Kwamishinan ilimin furamare da sakandare na jihar nan   Bello Abubakar Guiwa wanda ya sanarda umurnin rufe Makarantun, yace matakin nada manufar hana yaduwar cutar Corona dake cigaba da yin barazana a duk fadin duniya.Comments

19-03-20, 2:43 pm

Aliyu musa

Allah shi kara karemu daga dukkanin masifu duniya da lahira amin

Reply Like


Post Your CommentLocal News

Foreign News


© 2020 Copyright: visionfm.ng