Yan Boko Haram sun halaka sojoji da mazauna yankin Gubio


Mayakan sun kai harin ne a ranar Talata da rana, inda suka dinga bude wuta kan mazauna kauyen dake gudu, yayin da wasu kuma suka banke su da mota.

Babakura Kolo, wani mazaunin kauyen yace harin kamar ramako ne, ganin yadda mazauna kauyen suka kafa kungiya domin hana mayakan dake zuwa suna sace musu dabbobi.

Gubio na da nisan kilomita 80 daga Maiduguri. Ko a karshen mako mayakan boko haram sun kai hari kan dakarun Najeriya inda suka kasha 6 daga cikin su, yayin da sama da 40 suka bata.

Lamarin rashin tsaro na ci gaba da ciwa da dama daga cikin mazauna kauyuka a Najeriya tuwo a kwariya,yayinda gwamnati ke jaddada cewa ta na iya kokarin ta don kawo karshen yan kungiyar Boko haram.Comments

23-06-20, 5:58 am

Sabiu Abdu

Muna masu fatan maganar su na kokarin kawo karshen wannan hare hare daya addabi kasa baki daya musamman yankin arewacin kasar nan

Reply Like


Post Your CommentLocal News

Foreign News


© 2020 Copyright: visionfm.ng