Leganes tasha wuya hannun Barcelona daci 2-0


Har yanzu dai Barcelona ce gaba da jan ragamar gasar La-liga, bayan da ta doke Leganes da ci 2-0 a wasan mako na 29 da suka fafata ranar Talata a filin wasa na Camp Nou.
Matashin dan wasa haifaffen kasar Guinea-Bissau, wanda tauraruwar sa ke ci gaba da haskawa a fagen tamaula wato Ansu Fati ne ya zura kwallo kafin daga bisani Messi ya kara ta biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga wato fenariti.
Kyaftin din na Barcelona ya ciwa kungiyar sa ta Barcelona, da kasar sa ta haihuwa wato Argentina kwallaye 699, ya zura wannan kwallon ce bayan da dan wasan Leganes, Ruben Perez ya yi masa keta a cikin yadi na goma sha takwas.
a halin yanzu dai Barcelona ta sha gaban abokiyar hamayyarta Real tazarar maki biyar, sai dai kuma tanada kwantan wasa daya tsakanin ta da Valencia ranar Alhamis in mai duka yakaimu.Comments


Post Your CommentLocal News

Foreign News


© 2020 Copyright: visionfm.ng