El-Rufai Yana So A Dinga Yi Wa Masu Fyade Dandaƙa


Malam Nasir ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar ta bidiyo ta manhajar Zoom ranar Asabar.
An yi taron ne da nufin lalubo hanyoyin magance matsalar fyade da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.
Gwamnan ya ce cikin harshen Turanci wanda da shi aka gudanar da taron “Remove the tools”, wato a cire kayan aikin.
Sannan gwamnan ya ce a jiharsa ta Kaduna an samu karuwar fyade inda aka yi wa mutum 485 cikin kankanin lokaci a baya-bayan nan, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Taron yasamu halattar gwamnan jihar Kaduna, da ministar harkokin mata da shugabar hukumar NAPTIP da matan gwamnonin jihohin Niger da Kaduna da Kebbi.
Sauran mahalartan sun hada da ‘yan jarida da masu fafutuka da wakilan kungiyoyin Kare hakkin bil’adama da kuma lauyoyi.Comments


Post Your CommentLocal News

Foreign News


© 2020 Copyright: visionfm.ng