Gwamnatin Najeriya ta kara firashin man fetur daga N140.80 zuwa N143.80 a duka kan lita guda.


Hukumar kayade firashin ma fetur (PPPRA) ta sanar da karin kashi 16 cikin 100 na firashin man a wata sanarwa da shugabanta ya fitar a ranar Laraba.

A farkon watan Afrilu 2020, gwamnatin Najeriya ta sanar da ragin firashin man zuwa N123.50 a duk lita guda.
Sama da shekaru 20 yanzu firashin mai bai taba zama daidai ba a Najeriya. Wani lokaci ya hau wasu lokutan kuma a samu ragi.
Najeriya na daya daga cikin manyan kasashen da ke fitar da danyen man fetur amma dalilan da gwamnati ke bayarwa na hawa da saukan firashin a galibin lokuta watakila baya raba nasaba da yadda firashin ke sauyawa a kasuwar duniya.

‘‘Bayan nazari kan yadda kasuwar man ya kasance a watan Yuni da kuma duba kudaden da ‘yan kasuwa ke fitarwa wajen sayen man, muna shawarta karin kudin man daga N140.80 zuwa N143.80 a kan kowacce lita daga watan Yuli 2020,’’ yadda hukumar kayyade firashin mai na kasar PPPRA ta bayyana karin kenan a wata sanarwar da ta fitar ranar 1 ga watan Yuli, 2020.

Sanarwar ta shawarci dukkanin ‘yan kasuwa su sayar da man bisa sharudan PPPRA.Comments


Post Your CommentLocal News

Foreign News


© 2020 Copyright: visionfm.ng